Hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi dan wasan Chelsea, Mykhailo Mudryk da laifin karya ka’idojinta na hana amfani da kwayoyi masu kara kuzari, bayan da ya gaza tsallake gwajin kwayoyi, kuma a yanzu zai iya fuskantar hukuncin dakatar da shi na tsawon shekaru hudu, hukumar FA ta dakatar da dan wasan na kasar Ukraine, mai shekara 24 na wani dan lokaci a cikin watan Disamba bayan fitowar sakamakon binciken da aka yi a gwajin fitsari.
Chelsea ta kulla yarjejeniya da Mudryk daga Shakhtar Donetsk a watan Janairun 2023 kan kudi har fam miliyan 89, kuma yana da kwantiragi a kungiyar har zuwa watan Yunin 2031, Mudryk ya zura kwallaye 10 a wasanni 73 da ya buga a dukkanin gasannin da ya bugawa Blues (Chelsea).
- Sin Za Ta Samar Da Cibiyar Kasa Da Kasa Ta Gudanar Da Hada-hadar Kudin RMB Na Dijital
- An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana
Yan wasan da aka samu da amfani da kwayoyi masu kara kuzari da gangan ka iya fuskantar dakatarwa tsawon shekaru hudu a karkashin jagorancin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, a lokacin gwajin Mudryk ya ce bai taba yin amfani da wasu haramtattun abubuwa da gangan ba, tun ranar 28 ga watan Nuwamba bai buga wa Chelsea wasa ba.
Murdyk ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin Uefa Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin keta dokar hana kara kuzari, ta hanyar amfani da wani abu da aka haramta, wanda kuma ya sabawa doka ta 3 da 4 a kundin dokokin FA na hana kara kuzari.
Zuwa yanzu Chelsea ba ta ce komai ba dangane da tuhumar da akeyiwa Murdyk amma a watan Disamba ta ce, ta na fatan dan wasan nata yayi nasara duba da cewa “Mykhailo ya tabbatar da cewa bai taba yin amfani da haramtattun abubuwa da gangan ba” tace a cikin sanarwar, a karkashin dokokin FA, yan wasa sunada yancin bukatar ayi masu gwaji na biyu bayan an samu tabbacin amfani da kwayoyi masu kara kuzari a gwajin farko, amma idan gwajin na biyu ya zo daidai da na farko to za a yanke masu hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp