• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masarautar Gaya Ta Ƙwace Sarautar Wazirin Gaya Da Ta Bai Wa Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano

by Sadiq
5 months ago
Gaya

Masarautar Gaya da ke Jihar Kano ta ƙwace sarautar Wazirin Gaya daga hannun Alhaji Usman Alhaji.

Sanarwar hakan ta fito ne cikin wata wasiƙar da aka aike masa, kamar yadda Jami’in Yaɗa Labarai na Masarautar Gaya, Munzali Muhammad Hausawa, ya bayyana wa manema labarai.

  • Gwamnonin APC Sun Nemi Tinubu Ya Ƙirkiri ‘Yansandan Jihohi Don Yaƙar Matsalar Tsaro
  • Lakurawa Sun Sanya Dokar Hana Sayar Da Shanu A Kebbi

Sakataren Masarautar Gaya, Alhaji Bello Halilu, ya gode wa Alhaji Usman bisa gudunmawar da ya bai wa masarautar.

“Masarauta na godiya ƙwarai da gaske bisa sadaukarwarsa, goyon baya ga masarauta da ƙoƙarin raya al’adun Gaya,” in ji shi.

Alhaji Usman ya samu sarautar Wazirin Gaya ne a ranar 26 ga watan Janairu, 2020, bayan ya yi aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar.

LABARAI MASU NASABA

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu.

Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada.

Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan zarginta da karɓar bashi na dala miliyan 6.6.

Gwamnatin Kano ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ba gaskiya ba ne face tsantsar siyasa.

Ko da yake masarautar ba ta danganta ƙwace sarautar da wannan suka da Alhaji Usman ya yi ba, lokacin da aka ɗauki matakin ya haifar da zargi da cece-kuce a tsakanin jama’a.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
Labarai

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Manyan Labarai

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
Labarai

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Next Post
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo Ya Karyata Sauya Sheƙa Zuwa APC

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.