Barcelona ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao Nico Williams, amma kuma har yanzu akwai ƙalubalen da zasu fuskanta kafin ɗan wasan ya samu damar rattaba hannu a ƙungiyar ta Catalonia, ɗan wasan na ƙasar Sifaniya Williams, wanda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 167 da ya buga wa Bilbao, ya janyo hankalin ƙungiyoyin Arsenal da Bayern Munich a bana.
Amma ɗan wasan mai shekaru 22 ya amince da kwantiragin shekaru shida a Barcelona, wanda hakan zai sa ya hadu da abokinsa kuma abokin wasansa a matakin ƙasa Lamine Yamal a Nou Camp, Williams ya buƙaci Yamal da ya taimaka masa wajen zuwa Barcelona, bayan kakar da ya yi a Bilbao inda ya taimaka musu kai wa gasar zakarun Turai da kuma wasan kusa da na ƙarshe na gasar Europa duk a bana.
- Yamal Ya Saka Hannu A Sabon Kwantiragin Shekaru 6 A Barcelona
- Diaz Ba Na Sayarwa Bane – Liverpool Ta Fadawa Barcelona
Barcelona ta yi yunƙurin ɗaukar ɗan wasan Liverpool Luis Diaz a farkon bazara amma sai Liverpool ta nuna cewa darajar ɗan ƙasar Colombian ta kai fam miliyan 80, hakan ya sa Barca ta janye daga cinikin, Williams yana da yarjejeniyar da ta kai Yuro miliyan 62 (£53m) a kwantiraginsa a San Mames, wanda Barcelona ta nuna cewa za ta iya biya.
Daraktan wasannin Barcelona Deco ya gana da Williams da wakilansa a Ibiza a farkon wannan makon, inda aka amince da yarjejeniya ta fatar baki, Williams ne ya fara zura ƙwallo a raga a wasan ƙarshe na kofin European Cup da suka doke Ingila da ci 2-1 a Berlin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp