Rundunar ‘yansandan jihar Ondo ta gano maboyar wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne inda ta ta samu mutum biyu a gidan da ke yankin Epinmi Akoko.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar, DSP Ayanlade Olayinka ne ya bayyana cewa, wani matashi mai shekaru 25 mai suna Arohunmolase Idowu ne, ya fara shiga hannun ‘yan bangar yankin a ranar 18 ga watan Yunin nan da muke ciki.
- An Kaddamar Da Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka A London
- Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Ondo Da Shugaban Masu Rinjaye Sun Yi Murabus
Bayan an yi masa tambayoyi, da bincike akansa, ‘yansanda sun yi nasarar kama abokan aikin nasa da suke aikata muggan laifuka tare
Waɗanda ake zargin sun jagoranci jami’an tsaro zuwa wani gini mai nisa da ke cikin dajin inda ‘yansanda suka gano muggan makamai da suka hada da bindigu da aka kera a cikin gida da zarto da gatari da kuma layu.
An miƙa waɗanda ake zargi da kuma kayayyakin da aka ƙwato ga sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane domin ci gaba da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp