A cikin wani lokaci da ake cike na damuwa, sakamakon yawaitar rashin aikin yi, shaye-shaye da kuma damfarar yanar gizo tsakanin matasanmu, na samu damar ganin wani labari mai dadi daga Suleja, labari na ci gaba da kwazo daga hannun matasa da ya cancanci tallafi da goyon bayan kowa da kowa.
An gayyace ni a matsayin daya daga cikin masu sharhi a wani babban taron zamani da aka kira da; “The Digital Dominance Summit”, wanda taken sa ya kasance a matsayin ‘Gina Alamar Kasuwanci Mai Riba A Sabon Tattalin Arziki: Talla, Dabara Da Kuma Tasiri A Yanar Gizo.’ Kafin na amince da zuwa, shugaban taron kuma wanda ya kafa ‘Balpulse’, wato Coach Naseer Abdullahi, ya zo har gida ya bayyana min manufofin taron cikin kwarewa.
- Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa
- Amfani Da Karfin Gwamnati Kan ‘Yan Adawa Zai Jawo Wa Tinubu Illa A 2027 – Sule Lamido
A gaskiya ban cika sha’awar harkokin intanet ba, koda-yake na amfana da su kwarai da gaske. Amma da ya fara bayani mataki-mataki yadda suke tafiyar da ayyukansu, sai na kasa rufe baki saboda mamaki. Gaskiya matasa suna da fasaha da basirar da za su iya jan kansu daga kuncin talauci zuwa abin alfaharin al’umma.
Wannan taro dai, ya mayar da hankali ne a kan ‘affiliate marketing’, wanda ake nufi da “Talla mai cin gajiyar sakamako”. A nan, mutum na samun riba ta hanyar tallata kaya ko hidima na wani kamfani a kafafen sada zumunta ko yanar gizo. Da zarar wani ya saya daga hanyar da aka tallata, kai ma za ka samu naka kason. Yana da sauki wajen fahimta, amma babbar ribar tana tattare da cinikin kayan duk da mai tallar bai zuba jarin ko sisi ba. Wasu matasa a fadin Nijeriya, na samun miliyoyin kudi daga wannan fanni ba tare da karya doka ba.
Da farko, ni dai na je ne da niyyar yin kashedi a kan matsalar shaye-shaye da damfarar yanar gizo da matasa ke fadawa ciki dumu-dumu. Ko da kuwa, ba su ware lokaci domin wannan batu ba, ni dai ina shirin yin magana a kansa, domin kuwa shi ne babban kalubale a al’ummarmu. Amma abin mamaki, taron sai ya zame min wata hanya ta ganin wani sabon al’amari mai ban sha’awa daga matasanmu.
A can ne na hadu da wani matashi mai hazaka da kwazo, Faisal Ibrahim Abdullahi, wanda ya shaida min cewa; ya je Jihar Legas ne domin koyon fasahar ‘Epody Resin’, wato kera kayan ado da kayan daki na zamani da ake yi da sinadaran resin. Har yanzu, shi ne kadai daga yankinmu da ya mallaki wannan fasaha. Amma yana da burin koyar da sauran matasa muddin aka tallafa masa.
Na tsaya ina kallon kayan da ya nuna min na daki da ado, wanda na dauka cewa; ana yin su ne daga kasashen waje. Sai na ji cewa, “toh, dama a Suleja ake wannan?” Gaskiya wannan irin kwazo yana da bukatar tallafi, ba yabo kadai ba.
Bayan haka, taron ya kunshi gasa da horo a harkokin kasuwanci ta yanar gizo, inda matasa da dama suka samu kyaututtuka masu daraja daga ciki har da wata budurwa mai suna Blessing Paul da ta lashe kyautar mota da wasu da suka samu kyautar kudi.
Amma abin da ya dada daga min hankali shi ne, yadda galibin matasan da ke cin moriyar wannan dandali ba ’yan asalin Suleja ba ne. Wadanda suka fi mayar da hankali su ne daga wasu jihohi, suna rungumar dama da hannuwa biyu. Amma mu dai har yanzu muna ganin wadannan matasa kamar ‘yan damfara ne.
Wasu daga cikin masu rike da madafun iko ma sun yi watsi da gayyatarsu, idan ban da Mataimakin Shugaban karamar Hukumar Suleja da na Shiroro. Wasu daga cikin manyan sun yi wa su Coach Naseer mumunar fahimta, har suna yi musu kallon ‘Yahoo boys’ ne.
Ina ganin lokaci ya yi da za mu farka daga barci. Wadannan matasa suna kokari ne wajen gyara rayuwarsu ba tare da aikata laifi ba. Wajibi ne shugabanni da masu hannu da shuni da kuma masu zurfin tunani su rungumi irin wannan dandali, domin amfanin kowa da kowa.
Ga wasu daga cikin fa’idojin wannan dandalin talla na yanar gizo (affiliate marketing):
1- karfafa Matasa: Yana koya musu dogaro da kai da kuma dabarun kasuwanci.
2- Rage Aikata Laifuka: Matashin da ke da abin yi ba zai shiga yin shaye-shaye ko damfara ba.
3- Ci Gaban Al’umma: Nasarar mutum daya tana karfafa gwiwar wasu.
4- Samar Da Arziki: Wasu matasan da ke amfani da wannan dandali sun fara daukar ma’aikata, domin hannunsu ya fara maikon shuni.
5- Shiga Duniya: Matasanmu na iya fafatawa da sauran kasashen duniya daga cikin gida.
Don haka, ina kira ga Shuwagabannin Jihar Neja da na Suleja, ’yan kasuwa, manyan malamai da shugabannin gargajiya, da su bayar da goyon baya ga irin wannan yunkuri. Wannan dama ce ta fita daga kangin dogaro da gwamnati da kuma sauya tunanin cewa; dole sai an yi bariki ko kuma damfara kafin a samu kudi.
Haka zalika, kuna iya tallafa wa Faisal; domin ya koyar da matasa. Kuna kuma iya bayar da kayan aiki ko kudin horo. Amma mafi muhimmanci shi ne, ba su karfin gwiwa.
A nan ne, zan yi kira ga adali, manomin Gwamnan Jihar Neja; da ya bude wa wannan matashi kofar masana’antar Ladi Kwali, domin koyar da matasa wannan fasaha.
Yanzu duniya ta koma ta yanar gizo, wanda bai da fasahar zamani; kamar wanda bai iya karatu ba ne. Muna da zabi: mu goyi bayan irin su Coach Naseer da Faisal, ko kuma mu ci gaba da zargin su har su bar mu su tafi su samu nasara a inda ake mutunta fasaha irin tasu.
Daga Suleja nake kawo muku wannan labari mai dadi. Labarin harsashen nasara, ci gaba da inganci da ke kusa da mu, sai dai kash! Yawancinmu, ba ma ganin abin a haka.
Mu tashi tsaye. Mu goyi bayan kwazon matasanmu, kafin lokaci ya kure mana, ko wani ya zo ya amfana da su, mu kuma mu zauna muna ta faman korafi maras amfani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp