Ranar 21 ga watan Augusta, muhimmiyar rana ce ga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.
A wannan rana, jirgin kasan kasar Sin ya tashi daga tashar kasa da kasa ta Xi’an dake yammacin kasar, ya nufi birnin Hamburg na Jamus. Wanda ya zama karo na 10,000 da jirgin kasa na kasar Sin ya je Turai a bana.
A kuma ranar ce, aka fara fitar da jiragen kasa masu sauri na kasar Sin a hukumance, inda aka tura jiragen kasa masu amfani da lantarki da jerin jiragen gwajin layin dogon Jakarta zuwa Bandung, daga tashar ruwa ta Qindao ta kasar Sin.
Fitar da jirgin kasa mai sauri na kasar Sin, ya bude wani muhimmin babi. (Fa’iza Mustapha)