Dan takarar shugaban kasa a bababr jam’iyyar PDP, Atiki Abubakar, ya lashi takobin mika wa gwamnatocin jihohin ragamar kulawa da Jami’o’in gwamantin tarayyar, idan ya lashe zaben 2023.
Atiku, ya bayyana haka ne yayin wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a Jihar Legas.
- Zargin Cin Hanci: Babu Wani Shirin Tsige El-Rufai – Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna
- Masu Garkuwa Da Mutane Sun Shiga Komar ‘Yansanda, An Ceto Wadanda Suka Sace A DeltaÂ
An ruwaito Atiku ya ce kadarorin da Najeriya ta mallaka na iya karewa nan ba da dadewa ba.
“Daya daga cikin abubuwan da na shirya yi shi ne karfafa wa bangaren ‘yan kasuwa – na cikin gida da na waje – da su zuba jari a banagren ilimi domin Najeriya ba ta da kadarorin da za su dade tana sarrafa su kamar yadda take yi a yanzu.”
Ya kuma yi tsokaci kan talaucin da ya addabi yawancin ‘yan kasar, inda ya ce “tun bayan da Najeriya ta koma bisa turbar dimokradiyya a 1998 zuwa 1999, kasar ba ta taba samun kanta cikin tasko kamar wanda ta ke ciki ba a yanzu.”
Atiku ya yi alkawura da dama kan sauya wasu fasali na kadarorin Najeriya ciki har da sayar da Babban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC).