• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabbin Dokokin Haraji Za Su Fara Aiki A Janairun 2026 — Adedeji

by Sadiq
4 months ago
Haraji

Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (wadda a yanzu ake kira Nigeria Revenue Service — NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa sabbin dokokin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu za su fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2026.

Adedeji ya bayyana hakan ne a Abuja, a ranar Alhamis, bayan da shugaban ƙasa ya amince da sabbin dokokin gyaran haraji guda huɗu.

  • Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara
  • Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga

Ya ce wannan mataki babban ci gaba ne domin ƙirƙirar tsarin haraji na gaskiya, da kuma inganci.

Ya ce an tsara a bar tazarar watanni shida tsakanin sa hannun shugaban ƙasa da kuma lokacin da za a fara amfani da dokokin, domin a samu lokacin wayar da kai, da gyaran hukumomi don aiwatar da su yadda ya kamata.

Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka yi shi ne sauya sunan hukumar daga FIRS zuwa Nigeria Revenue Service (NRS).

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

Adedeji ya ce har zuwa sa’o’i biyu kafin sanarwar, sunan hukumar shi ne FIRS, amma yanzu sunan ya koma NRS.

Ya bayyana cewa sabuwar hukumar ba za ta tsaya kan tattara haraji kawai ba, domin yanzu tana damar tattara sauran kuɗaɗen shiga da ba na haraji ba.

Hakazalika, za ta yi aiki cikin ’yanci tare da bin ƙa’idojin bayyanan aiki da bin diddigin nasarori.

Ya ƙara da cewa sabuwar hukumar za ta mayar da hankali sosai wajen cimma nasarori, kuma za ta yi aiki da ƙwarewa kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya.

Shi ma shugaban kwamitin gyaran haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa ko da kuwa doka na da kyau, idan ba a aiwatar da ita yadda ya kamata ba, ba za ta amfanar da ƙasa ba.

Ya ce yanzu shugaban ƙasa ya umarce su da su fara aiki yadda ya kamata.

Oyedele ya ja hankalin jama’a cewa wannan gyara ba zai yi nasara ba sai kowa ya bayar da gudunmawarsa.

Ya ce gwamnati kaɗai ba za ta iya aiwatar da wannan sauyi ba.

Dole ne a samu haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki, ƙungiyoyin fararen hula, ƙwararru, da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa.

Shugaba Tinubu tun da farko ya ce dokokin harajin an tsara su ne don gina ƙasa, tare da kawar da ɓarna da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

Wannan gyaran haraji yana cikin babban shirin gwamnatinsa da ke neman kyautata yanayin kasuwanci, ƙara samun kuɗaɗen shiga, da kuma ganin ci gaba ya waanzu a faɗin ƙasar.

Yanzu da aka sa ranar fara amfani da dokokin a Janairun 2026, hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki suna da lokaci don shirya duk abin da ya kamata domin tabbatar da cewa sabbin dokokin harajin sun cika burinsu na kawo ci gaba ga ƙasa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
Manyan Labarai

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Next Post
Afirka CDC Ta Yaba Da Hadin Gwiwa Kan Kiwon Lafiya Da Kasar Sin

Afirka CDC Ta Yaba Da Hadin Gwiwa Kan Kiwon Lafiya Da Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.