Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha don ziyarar aiki.
Firaministan Habasha, Dokta Abiy Ahmed Ali, ne ya gayyace shi.
- Afirka CDC Ta Yaba Da Hadin Gwiwa Kan Kiwon Lafiya Da Kasar Sin
- Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…
A lokacin wannan ziyara, Shettima zai halarci ƙaddamar da Shirin Kare Muhalli na ƙasar Habasha.
Wannan shiri ne na musamman da aka ƙaddamar don daƙile sare itatuwa, kare halittu, da kuma yaƙi da sauyin yanayi.
An shirya shuka itatuwa biliyan 20 cikin shekaru huɗu a ƙasar.
Shettima zai kuma ziyarci manyan masana’antu da gonaki a sassa daban-daban na Habasha.
Masana’antun sun haɗa da Adama Industrial Zone, Mojo Poultry Farm, Shera Dibandiba Mojo Family Farm, Lume Avocado Nursery, da Bishoftu Pea Youth Farm.
Wannan ziyara na da nufin ƙarfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Habasha, musamman a fannin noma da masana’antu.
Firaminista Abiy zai kuma shirya wata liyafa ta musamman a Fadar Shugaban Kasar domin girmama Shettima da tawagarsa, a matsayin alamar ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Nijeriya da Habasha na da daɗaɗɗen tarihin aiki tare, musamman a fannonin tsaro, kiyaye zaman lafiya da kuma haɗin gwiwar tattalin arziƙi.
Wannan ziyara na da burin ƙarfafa wannan dangantaka da kuma samar da damar haɗin gwiwa a fannin sauyin yanayi, wadatar abinci, da ci gaban masana’antu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp