Jami’an kamfanin mai na ƙasa (NNPC) sun ƙi halartar binciken majalisar dattawa kan batan Naira tiriliyan 210 da suka ɓace a cikin bayanan kuɗin kamfanin daga 2017 zuwa 2023.
Duk da cewa babu wani babban jami’in NNPC ko masu duba lissafin su da suka halarci taron, wakilan EFCC, ICPC da DSS sun halarta. Majalisar ta ba NNPC kwanaki 10 na ƙarshe don su bayyana.
- Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi
- Majalisa Ta Yi Allah-wadai Da Kashe Wasu Matafiya ‘Yan Kaduna 13 A Jihar Filato
A cikin wasiƙar da CFO Dapo Segun ya sanya hannu, NNPC ta nemi a ba ta wata biyu don tattara bayanai, inda ta bayyana cewa mambobin hukumar gudanarwa da manyan jami’ai suna tafiyar aiki.
Amma shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ya yi watsi da buƙatar, yana mai cewa: “Ba za mu karɓi wannan uzurin ba. NNPC ya kamata ta bayyana a nan a ranar 10 ga watan Yuli don amsa tambayoyinmu.
Sanata Abdul Ningi daga Bauchi ya goyi bayan hukuncin, ya kuma bukaci babban darakta Bayo Ojulari ya jagoranci tawagar NNPC a lokacin da za su dawo zaman majalisa.
“Idan sun ƙi zuwa, za mu yi amfani da dukkan ikonmu na tsarin mulki,” in ji Wadada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp