An samu radani kan bukatar yi wa ADA rajisata domin zama jam’iyyar siyasa a wurin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC). Ana ganin cewa kungiyar na samun tallafi daga kungiyar hadin gwiwa ta Nijeriya (NNCG).
A cikin wata wasika da aka rubuta a ranar 19 ga Yuni, kungiyar da ke da kudirin zama jam’iyyar ta bayyana cewa ta cika duk wata ka’ida na kundin tsarin mulkin kasar nan da ka’idojin INEC wajen zama jam’iyyar siyasa da ta cancanci yi mata rajista.
- Shugabannin PDP Sun Ziyarci INEC Kan Neman Sanin Ka’idojinta
- Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu Rajista
Sai dai kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa shi da sauran shugabannin a cikin NNCG sun amince da ADA ta zama sabon jam’iyyar don kalubalantar Shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC a yunkurin sake zabe sa a zaben 2027.
Mashawarcin Atiku kan kafofin yada labarai na zamani, Demola Olarenwaju, ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin shugabannin NNCG, don haka ba a cimma wani matsaya na karshe ba kan yiwuwar amincewa da ADA.
Olarenwaju ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa, “Wani kungiya na kokarin samun rajisata domin zama jam’iyya, kamar kowanne dan Nijeriya, amma tana bukatar yin kawance. Ba a karba kawancen ADA ba, idan lokaci ya yi, za a sanar da jama’a game da batun da kuma matakin da za a dauka. Ku yi hakuri da wannan.”
Haka shi ma, shugaban ADC, Cif Ralph Okey Nwosu, ya karyata amincewa da ADA, yana mai cewa batun zama jam’iyya kawance lokaci ya riga ya shude. Ya ce sake bijiro da kawance a hukumance ya faru ne wannan makon, bisa ga shawarar daga dukkan masu ruwa da tsaki.
A cewar wani rahoto, NNCG ta yi rajistar ADA a hukumance ga INEC. Wasikar neman rajistar ADA daga INEC an sanya hannu a kai daga shugaban kungiyar na wucin gadi, Cif Akin A. Rickets, da sakataren kungiyar na wucin gadi, Abdullahi Elayo.
Hadakar ta kuma gabatar da takardu masu muhimmanci, daga cikin su akwai kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka bayar da manufifinra da tambari da kuma bayanan taron kafa ta.
Wasikar ta bayyana cewa alamar masara tana wakiltar juriya da tsafta da muhimman tunani da suke fatan inganta.
“Mun kara hadawa da manufofinmu wacce ta kunshi bayanai game da ra’ayin jam’iyyarmu da kundin tsarin mulkinmu wanda ke bayar da doka da ke bayyana ainihinmu, tsarinmu, da mamufarmu,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp