Ofishin kula da aikin harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ba da labari cewa, jiya Alhamis da karfe 9 da mintuna 29 na dare agogon Beijing, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, wato Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie sun cimma nasarar fitowa daga akwatin gwaji na Wentian, yin tattaki a waje na tsawon sa’o’i 6.5, da kuma komawa akwatin, bisa taimakon na’urori masu hannun injin dake tashar sararin samaniya da jagorancin masu nazarin kimiyya da fasaha dake doron kasa.
Yayin da suke aiki a waje, Chen Dong da Chen Zhongrui sun cimma nasarar hada na’urorin kiyaye tashar sararin samaniya daga sassan wasu na’urorin da aka daddasa a sararin samaniya, da binciken na’urorin dake waje da tashar da daidaita wasu matsaloli da sauransu.
Ya zuwa yanzu, ‘yan sama jannatin suna tafiyar da ayyukansu bi da bi yadda ya kamata, daga baya kuma za su yi nazari da gudanar da aikin gwaji kan bangaren kimiyyar rayuka da tushen samuwar karamar fizga ko “jazibiyya” da kimiyyar albarkatun sararin samaniya da aikin jinya a sararin samaniya da sabbin kimiyya da fasahohin zirga-zirga a sararin samaniya da sauransu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp