Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye kujerarsa a matsayin Shugaban Jam’iyyar.
Ajiye kujerar tasa wani yunƙurin ne na jam’iyyar mai mulki don rage matsalolin da ta ke fuskanta daga mambobin yankin Arewa ta Tsakiya, waɗanda tun da daɗewa suke neman a dawo da shugabancin jam’iyyar zuwa yankinsu.
- An Watsa Shirin “Yawon Bude Ido A Tuscany” Da Cmg Ya Gabatar A Italiya
- Yunwa Da Talauci Ne Ke Barazana Ga Harkar Tsaro A Kasar Nan — NSA, CDS
Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa ɗaya daga cikin mataimakan shugabannin jam’iyyar na ƙasa zai bayar da riƙon shugabanci har zuwa lokacin da za a zaɓi sabon shugabanta a babban taron jam’iyyar da aka shirya yi a watan Disamban 2025.
“An daɗe ana matsa masa lamba. Manya da mambobin jam’iyya daga Arewa ta Tsakiya ba su daina matsawa ba domin ganin an dawo da kujerar,” in ji wata majiya daga cikin jam’iyyar.
“Yanzu Ganduje ya amince ya sauka domin amfanin jam’iyyar, musamman yayin da ake shirin fara tsare-tsaren tunkarar zaɓen 2027.”
Ganduje, wanda ya kasance Gwamnan Jihar Kano daga 2015 zuwa 2023, ya zama shugaban APC a watan Agustan 2023 bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu daga yankin Arewa ta Tsakiya.
Tun daga wannan lokacin ne wasu daga cikin mambobin jam’iyyar suka fara sukar jagorancinsa, suna ganin naɗa shi ya karya tsarin raba muƙamai na cikin gida da jam’iyyar ke bi.
Dama tuni wasu manyan dattawan jam’iyyar da shugabannin yankuna daban-daban suka bayyana rashin jin daɗinsu, inda suka dk ga kira ga jam’iyyar da ta gyara wannan tsari.
Majiyoyi sun ce saukar Ganduje za ta samar da haɗin kai a cikin jam’iyyar, da kuma gyara matsalolin rabon muƙamai don sake farfaɗo da APC kafin babban zaɓen 2027.
A halin yanzu, babu wata sanarwa da Ganduje ko jam’iyyar APC ta fitar kan murabus ɗinsa.
Murabus ɗin na Ganduje na nuna wani babban sauyi a shugabancin jam’iyyar APC tun bayan hawan mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp