A makon da ya gabata ne wasu kasashen Afirka uku suka gabatar tare da amince da kasafin kudinsu na shekarar da muke ciki, a wani mataki na bunkasa tatattalin arzikin kasashen.
Kasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda sun gabatar da kasafin kudin da ya mayar hankali kan zabuka da tattalin arzikin kasashen.
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi
- Kasashen Afirka 10 Da Za Su Samu Bunkasar Tattalin Arziki A 2024
A kowace shekara kasashen Afirka kan kara yawan kasafin kudadensu, watakila sakamakon raguwar darajar kudaden kasashen.
Alal misali Nijeriya – wadda ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka – kasafin kudin kasar na bana ya zarta na shekarar da ta gabata da kusan rabi.
A makon da ya gabata ne wasu kasashen Afirka uku suka gabatar tare da amince da kasafin kudinsu na shekarar da muke ciki, a wani mataki na bunkasa tatattalin arzikin kasashen.
Kasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda sun gabatar da kasafin kudin da ya mayar hankali kan zabuka da tattalin arzikin kasashen.
Galibi kasafin kudin kasahen Afirka kan mayar da hankali wajen cimmma muradunsu na tattalin arziki da ci gaba.
Kasafin kudin kasashen Afirka na 2025 na kunshe da muradun ci gaba da bunkasar abubuwan more rayuwa da kuma ingantuwar al’amuran yau da kullum a kasashen.
Kunshin kasafin kudin kasashen Afirka na 2025 ya ware gagarumin kaso a fannin inganta abubuwan more rayuwa da ayyukan kyautata rayuwar al’umma da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen.
Kowace shekara kasashen Afirka na ware makudan kudade a kasafin kudadensu.
A wannan makala mun zakulo kuku kasashen Afirka 10 da suka fi girman kasafin kudi, kuma mun yi kiyasin da Dala domin samun saukin lissafi.
- Afirka ta Kudu – (Dala biliyan 141.4)
Kasar Afirka ta Kudu ce kan gaba wajen ware makudan kudade a kasafin kudi a Afirka a 2025.
A wannan shekara kasar ta ware Dala biliyan 141.4 a matsayin kasafin kudiinta.
Kasafin kudin ya fifita fannin abubuwan more rayuwa da ayyukan bunkasa rauyuwar jama’a da ci gaban tattalin arziki.
- Algeria – (Dala biliyan 126)
Kasar Algeria ce ke matsayi na biyu a yawan kasafin kudi a nahiyar Afirka a 2025. Kasar – wadda ke arewacin Afirka – ta ware Dala biliyan 126 a kasafin kudinta, inda tafifita fannnonin makamashi da tsaro.
- Masar – (Dala biliyan 91)
Masar ce ta uku cikin jerin, mai adadin kudi har Dala biliyan 91, inda ta ware kaso mai yawa zuwa fannonin ilimi da lafiya da ayyukan da za su amfani jama’a.
- Morocco – (Dala biliyan 73)
Kasar Morocco – da ita ma ke yankin arewacin Afirka ta kasance a mataki na hudu.
Morocco ta ware Dala biliyan 73 a kasafin kudinta na shekarar 2025.
- Angola – (Dala biliyan 37.847)
Angola – arzikin man fetur – ce a matsayi na biyar cikin jerin kasashen Afirka da suka fi karfin kasafin kudi.
Kasar – wadda ke yankin kudancin Afirka – ware Dala biliyan 37.847 domin kasafin kudinta na shekarar da muke ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp