Shugaba Bola Tinubu ya nuna baƙin ciki kan rasuwar tsohon minista kama attajirin ƙasar Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a ranar Asabar yana da shekaru 94, inda ya bayyana mutuwar a matsayin “babban rashi ga Nijeriya.”
A wata sanarwa, Tinubu ya yaba wa Ɗantata saboda gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa da kuma haɗa kan al’umma ta hanyar kasuwancinsa.
- Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu
- Za a Binne Ɗantata A Madina, Za Ai Yi Sallar Ga’ibi A Kano
Tsohon kwamishinan tsare-tsare na jihar Kano ya kuma kasance sananne wajen ayyukan agaji musamman a fannin ilimi da kiwon lafiya.
Shugaban ya tuna da shawarwarin da Ɗantata ya ba shi a lokuta daban-daban, yana mai cewa sun taimaka masa sosai.
Ya kuma aika ta’aziyya ga dangin marigayin da gwamnatin jihar Kano.