Sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Ali Bukar Dalori, ya bayyana cewa ba su damu da yunƙurin da jam’iyyun adawa ke yi na haɗa kai domin ƙalubalantar jam’iyyar ba.
Ya ce wannan ba abu ne da zai tayar masu da hankali ba.
- Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya
- Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu
A wata hira da ya yi da BBC, Dalori wanda ya hau kujerar shugabancin APC a ranar Litinin, ya ce babban burinsa shi ne haɗa kan mambobin jam’iyyar da kuma tabbatar da adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.
“Zan yi ƙoƙari na sasanta duk wanda ke da matsala a jam’iyyar. Za mu zauna da su, ko kuma mu tura wakilai domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai,” in ji shi.
Dalori ya ce siyasa na buƙatar mutane da kulawa, kuma zai jajirce wajen ganin APC ta ci gaba da kasancewa a sahun gaba.
Game da babban taron jam’iyyar na ƙasa, Dalori ya ce har yanzu ba su yanke shawarar lokacin gudanarwa ba, domin yana jiran ra’ayin manyan jiga-jigan jam’iyyar.
“Dole ne mu nemi shawarar manyan jam’iyyar kafin mu yanke hukunci,” in ji shi.
Yayin da ake cewa APC na fama da matsaloli a wasu jihohi musamman a Arewa maso Gabas, wanda shi ne yankin da Dalori ya fito, ya ce irin hakan abu ne da aka saba da shi a siyasa.
“Siyasa haka ta ke, amma duk da haka muna da haɗin kai kuma muna aiki tare.”
Dalori ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan adawa da suka sauya sheƙa zuwa APC, sun yi hakan ne saboda sun tsorata da makomarsu a jam’iyyunsu.
“Sun san ba za su ci zaɓe a can ba, don haka suka zo domin samun damar cika muradunsu,” in ji shi.
A ƙarshe, ya ce yunƙurin haɗa kan jam’iyyun adawa ba zai yi wani tasiri a kansu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp