Yau Laraba, Hukumar Kula da Fasaha ta Kasar Sin (MIIT) ta ba da rahoton yanayin tafiyar masana’antar manhajoji ta kasar daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar 2025 da muke ciki.
A cewar rahoton, masana’antar manhaja da hidimar fasahar sadarwa ta Sin tana gudana yadda ya kamata. Da farko, yawan kudaden shiga da aka samu kan sana’ar manhaja ya karu karara. Daga Janairu zuwa Mayu, adadin ya kai kudin Sin yuan triliyan 5.5788, wato ya karu da kashi 11.2% idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara.
Na biyu, ribar da aka samu a fannin kuma ta habaka da kashi 10% ko fiye. Daga Janairu zuwa Mayu, jimilar ribar da aka samu a bangaren sana’ar manhaja ta kai kudin Sin yuan biliyan 672.1, wadda ta karu da kashi 12.8 cikin dari kan na makamancin lokacin bara.
Na uku, yawan manhajojin da aka fitar ya ci gaba da karuwa cikin inganci. A cikin watanni biyar na farkon bana, darajar kayayyakin manhaja da aka fitar ya kai dalar Amurka biliyan 22.71, adadin da ya karu da 3.3% bisa na makamancin lokacin a bara. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp