Gwamnatin Kasar Amurka ta rattaba hannun yarjeniya da Gwamnatin Tarayya don dawowa da Nijeriya Dala miliyan 23 da ake zargin tsohon shugaban mulkin soji, marigayi Sani Abacha da wawure.
Yarjejeniyar wadda aka sa hannu a yau Talata a ofishin Ministan Shari’a kuma Atoni-Janar na kasa Abubakar Malami, a jawabin ministan ya ce, an dauki matakin dawo da kudaden ne da aka yi wa lakabi da Abacha-5.
- Tsarin Tantance Ingancin Rigakafin Sin Ya Kai Sabon Mataki Na Nagarta
- An Yi Wa Mawaki Eedris Abdulkareem Dashen Koda
Malami, ya ce an samu nasarar ne bayan tattaunawa da kuma gudanar da ganawa a tsakanin sashen don tabbatar da adalci da kuma hukumar binciken aikata manyan laifuka ta kasar Birtaniya.
Ya ci gaba da cewa, idan kudaden sun iso Nijeriya za a yi amfani da su don a kammala gyaran babbar hanyar Abuja zuwa Kano da kammala aikin dadar Neja.
A nata jawabin jakadae Amurka a Nijeriya, Mary Leonard, ta ce sashen na tabbatar da adalci na Amurka da FBI ne suka kwace kudaden saboda taka dokar Amurka da Abacha da abokan harkallarsa suka yi na safarar kudaden ta haramtacciya hanya zuwa tare da jibge su a asusun bankuna da ke a kasar Birtaniya.
Mary, ta ce idan aka hada da dala 311.7 miliyan da aka kwato tare da mayarwa zuwa Nijeriya ta hanyar taimakawar Bailiwick na Jersey da kuma Gwamnatin Tarayya a 2022, a jimlace Amurka ta dawo wa da Nijeriya sama da dala miliyan 334.7 .311.