Wata Kotun Majistare da ke jihar Kano ta yanke wa fitaccen ɗan TikTok, Umar Hashim da aka fi sani da Tsulange, hukuncin ɗauri na shekara ɗaya bisa laifin aikata abinda ya saɓa da tarbiyya a bainar jama’a.
Alƙaliyar kotun, Hadiza Muhammad Hassan, wadda ke zaune a Gyadi Gyadi, ta samu Tsulange da laifi na zubar da mutunci a idon jama’a bayan gabatar da hujjoji da shaidu. Ta bayyana cewa an tabbatar da cewa ɗan TikTok ɗin ya aikata laifin ne cikin gangan.
- Ɗan TikTok Tsulange Ya Shiga Hannu Bisa Wanka Da Rigar Mama A Titi
- Kotu Ta Tura Ɗan Tiktok Gidan Yari Kan Shigar Mata Da Kalaman Batsa A Kano
A hukuncin da ta yanke, ta ba da umarnin da a ɗaure shi na tsawon shekara guda, ko kuma ya biya tarar Naira 80,000 a matsayin madadin ɗaurin. Haka kuma, kotun ta umarce shi da ya biya hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Naira 20,000 don rage kuɗin bincike da shari’ar da aka yi.
Rahoton LEADERSHIP ya nuna cewa an gurfanar da Tsulange ne a watan Yuni 2025 bayan hukumar ta kama shi kan wani faifan barkwanci da ya ɗauka yana wanka a titi yana sanye da kayan mata a matsayin wani ɓangare na wasan kwaikwayo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp