Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta tsaida ranar 16 ga Agusta don gudanar da zabe cike gibi a mazabe 16 da ke a jihohi 12 na tarayyar Nijeriya.
Hukumar ta kara da cewa za ta tura jami’ai 30,451 don gudanar da zaben, kuma ta sanar da ci gaba da yin rajistar zabe a duk fadin kasar, daga ranar 18 ga watan Agusta.
- Sin Ta Bai Wa Habasha Kayayyakin Tallafin Jinya
- Ɗan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana wannan a taron tattaunawa tare da jam’iyyar siyasa a Abuja, ya ce bisa ga korafe-korafen da ke fitowa daga jam’iyyun adawa na cewa wadanda suka dade suna rike da mukamai sukan hana su samun damar amfani da wuraren gwamnatin, ciki har da kafofin watsa labarai na gwamnati.
Ya ce daga yanzu, hukumar za ta yi aiki tare cibiyar hadakar jam’iyyu (IPAC) da hukumar kula da tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), don daukar matakin shari’a kan masu irin wannan laifi.
Yakubu ya ce, “Yayin da ake fara ayyukan yakin neman zabe a Jihar Anambra, ina so in jawo hankali ga masu korafe-korafe musamman jam’iyyun adawa game da Rashin bayar da damar shiga wuraren gwamnati don gudanar da ayyukan zabe. Wadannan sun hada da kafofin yada labarai na jihar, gine-ginen gwamnati don taruka da kuma wuraren da ake kibe don yin gangamin da taruka.”
“A wasu lokutan, ana cajin kudi masu yawa waje tallace-tallace. Wadannan abubuwan na cikin rashin bin doka a cikin dokar zabe ta 2022 wadda ke hana amfani da matsayi don musguna wa kowanne jam’iyya ko dan takara.
“Hukumarmu za ta yi aiki tare da cibiyar hadakar jam’iyyu (IPAC), kuma za mu kara karfafa hadin gwiwarmu da hukumar kula da tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), don daukar matakin doka idan aka samu shaidu masu karfi na karya doka.
“Game da zaben cike gibi kuwa, bari in ba ku takaitaccen bayani kan lamarin. A cikin shekaru biyu da suka gabata tun lokacin kaddamar da majalisun kasa da na jihohi a watan Yunin 2023, an samu kujerun ‘yan majalisa da babu kowa wanda ake bukatar yi zabe a fadin kasar nan.
“Idan za ku iya tunawa cewa a watan Fabrairu na shekarar da ta gabata, hukumar ta gudanar da zaben cike gurbi domin cike kujeru guda tara da aka samu sakamakon mutuwar ko murabus na ‘yan majalisun tarayya na jihohi. Tun daga wannan lokacin, an samu karin gurabe a fadin kasar nan.
“A saboda haka, hukumar ta fitar da ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, don gudanar da zaben cike gibi a mazabu 16 a da ke jihohi 12 na kasar nan, wanda ya kunshin adadin masu zabe 3,553,659 da aka yi wa rajista, wanda aka rarraba a cikin kananan hukumomi 32, wuraren zabe 356 da kuma rukunin zaben 6,987. Hukumar za ta tura jami’ai 30,451,” in ji shugaban INCE.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp