Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ya karyata jita-jitar cewa zai sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Duk da raɗe-raɗin da ke yawo, Gwamna Adeleke ya tabbatar da cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP kuma shi ne jagoran jam’iyyar a jihar.
Gwamnan ya sake jaddada cewa yana mai da hankali ne wajen aiwatar da shirye shiryen gwamnatinsa na ƙuduroei biyar, kuma ya roƙi jama’ar jihar da su yi watsi da labaran ƙarya, yana mai alƙawarin ci gaba da samar da kyakkyawan shugabanci a tafarkin dimokuraɗiyya.
- Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Adeleke A Matsayin Gwamnan Osun
A lokaci guda, jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta kuma ƙaryata jita-jitar cewa Gwamna Adeleke ko wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar za su sauya sheka zuwa APC. Shugaban PDP na jihar, Hon Sunday Bisi, ya bayyana cewa wannan jita-jitar ‘yan adawa ce da suka ƙirƙira don su tayar da fitina, yana mai cewa jam’iyyar PDP a jihar tana da ƙarfi da haɗin kai, kuma za ta ci gaba da ƙoƙarin ceto al’umma da gina jihar Osun.
Bisi ya ƙara da cewa, “Mun fahimci yadda wannan jita-jita ta sa damuwa da tashin hankali a tsakanin mambobinmu da magoya baya. Amma muna tabbatar da cewa PDP ba ta karaya ba, har yanzu muna tare da Gwamna Adeleke wajen ganin an kawo ci gaba a Osun.”
Ya kuma roƙi jama’ar jihar Osun da su yi watsi da wannan jita-jita, su ci gaba da mara wa gwamnatin Gwamna Adeleke baya domin ganin an samu ingantaccen shugabanci a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp