Wasu mutane tara sun rasa rayukansu a wani hari da aka kai garin Malamfatori da ke karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.
Harin ya kuma jikkata wasu mutane huɗu da raunuka a wannan gari da ke kan iyaka, wanda ke da nisan kilomita 272 daga Maiduguri, babban birnin jihar.
- Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
- Ministan Tsaro Ya Yi Gargadin Sake Dawowar Boko Haram Na Barazana Ga Nijeriya
A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Borno ta fitar a ranar Lahadi, wanda Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Sugun Mele, ya wakilta, ya jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su tare da ba su tallafin kuɗi.
Ya ce, “Mun zo ne a madadin Mai Girma Gwamna Babagana Umara Zulum, wanda ke wajen kasar nan a sakamakon wata tafiya ta aiki da ya yi, domin jajanta wa al’ummar Malam Fatori bisa wannan mummunan hari da aka kai kwanan nan. Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Borno tare da sojoji za su yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron garin.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp