Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), ba ta da wasu dalilai na ci gaba da yajin aikin da suke yi.
Badaru ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manyan sakatarori, daraktoci da shugabannin ma’aikatu da na kananan hukumomi a dakin taro na Sir Ahmadu Bello da ke Dutse.
- Mai Mala Buni Ya Bai Wa ‘Ya’yan Sheikh Aisami Da Aka Yi Wa Kisan Gilla Aiki
- Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba – Kwankwaso
Gwamnan, ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan yajin aikin da ASUU a Jami’ar Sule Lamido ke yi, reshen Kafin-Hausa a Jihar Jigawa.
Ya bayyana cewa ASUU a jami’ar mallakar gwamnati ba ta da dalilin ci gaba da yajin aikin.
“Ban ga dalilin da zai sa jami’o’in jiha su ci gaba da yajin aikin saboda kamar yadda gwamnatin jihar ta riga ta biya musu bukatunsu bai kamata suke yin yajin aiki ba.
“Kusan kashi saba’in cikin dari na malamai ‘yan asalin jihar ne da suke tunanin nuna kauna da damuwa ga ilimin matasan gobe,” in ji shi.
Gwamna Badaru ya bukaci kungiyar da ta yaba da jajircewar gwamnati kada a yi amfani da su wajen yakin da bai shafe su ba.
Don haka ya bukaci dattawa da sauran masu ruwa da tsaki a jihar su sa baki a yajin aikin da ake yi.
ASUU ta shiga yajin aikin ne a ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022, kan batun takaddamar tsarin biyan albashi na IPPIS, sai dai jami’o’in gwamnatin jihar ba su da alaka da IPPIS tunda albashinsu baya zuwa daga gwamnatin tarayya.