Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta janye yajin aikin da ta fara bayan da gwamnatin tarayya ta biya albashin mambobinta na watan Yunin 2025.
Shugaban ASUU na Jami’ar Abuja, Dr. Sylvanus Ugoh, ya shaida wa LEADERSHIP a ranar Talata cewa ƙungiyar ta yanke shawarar janye yajin aikin ne bayan da aka fara biyan mambobinta albashin watan Yuni.
Ya ce, “Albashin Yuni na mambobinmu ya fara shigowa kafin wa’adin da muka bayar ya cika. Saboda haka, ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin da ta fara.”
Wannan matakin ya hana yiwuwar rufe jami’o’i a faɗin ƙasar nan.
Tun da farko, shugabancin ASUU na ƙasa ya umarci rassanta da su dakatar da aiki idan aka ƙi biyan albashin Yuni a kan lokaci.
Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta.
ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun.
Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba.
“Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen mutanen da ke da alhakin sakin kuɗin ne,” in ji Piwuna.
Ya ƙara da cewa sauyi tsarin biyan albashi daga IPPIS zuwa GIFMIS ya ƙara jefa malamai cikin wahala.
ASUU ta ce duk wata Jami’a da ba a biya malamanta albashin Yuni kafin 7 ga Yuli ba, to, ya kamata su fara yajin aiki nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp