A ƙalla mutane goma sha uku (13) ne suka rasa rayukansu a daren Talata sakamakon harin da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kai a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru a kauyukan Magoro, da Kumbashi da Bangi — shalƙwatar ƙaramar hukumar. Cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai ƴan sa-kai guda uku da kuma wani jami’in ƴansanda da ke bakin aiki a yankin.
- Neja: Cikin Wata 10 Ibtila’i Ya Lakume Rayuka Sama Da 400 – NSMA
- Firaminsitan Sin: Dole Ne Hadin Gwiwar Brics Ya Gaggauta Kafa Ka’idar Ciniki Da Tattalin Arzikin Duniya Mai Adalci Da Bude Kofa
Shaidu sun ce ƴan bindigar sun shigo ƙauyukan ne a kan babura kimanin 150 ɗauke da makamai masu linzami, inda suka buɗe wuta ba tare da kakkautawa ba, wanda hakan ya haifar da mutuwar mutane 13 da kuma jikkatar wasu da dama.
Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Alhaji Abbas Kasuwa Garba, ya tabbatar da kai harin, koda yake ya ce har yanzu ba zai iya tantance adadin waɗanda suka mutu ba. Ya bayyana cewa lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin fargaba, yayin da ƴan bindigar ke cigaba da kai farmaki daga gari zuwa gari.
Ana ci gaba da samun ƙarin bayani kan
lamarin…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp