Tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ba mutum ba ne mai son dukiya ko abun duniya ba.
Gowon ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 9 ga watan Yuli, 2025, yayin ƙaddamar da wani sabuwar littafi mai suna “According to the President: Lessons from a Presidential Spokesman’s Experience” wanda Garba Shehu ya rubuta, tsohon mai magana da yawun Buhari.
- UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 13 A Neja
A yayin taron, Gowon ya yaba da halin Buhari na kishin ƙasa da kuma yadda yake kiyaye mutuncinsa.
Gowon ya ce: “Na san Janar Buhari sosai. Mutum ne da ke da cikakken imani don ci gaban Nijeriya.
“Ba mutum ba ne mai son dukiya ko abun duniya ba. Kuma yana ƙoƙari sosai wajen kare mutuncinsa. Gaskiya ne, rayuwarsa mai sauƙi ce.”
Ya kuma yaba wa Garba Shehu bisa rubuta littafin, yana mai cewa hulɗa da jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen tafiyar da mulki da kuma gina ƙasa.