Kwanaki biyu da suka gabata, kafofin yada labaran Najeriya da dama sun buga bayanin da wani shahararren dan siyasa mai suna Dakuku Peterside ya rubuta, mai taken “Mene ne Najeriya za ta iya koya daga ci gaban kasar Sin a fannin samar da wutar lantarki?” Kasidar ta yi nuni da cewa, a shekarar 2000, ma’aunin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya kai fiye da tiriliyan 1.3 KWH, kusan kashi daya bisa uku na lantarki da kasar Amurka ta samar. Sai dai ya zuwa shekarar 2024, karfin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya zarce KWH tiriliyan 10, kusan ninki biyun na Amurka, kuma a daga cikin lantarkin, wanda aka samu daga makamashi mai tsabta ya kai kimanin kaso 55%. To, ko ta yaya kasar Sin ta cimma nasarar hakan? Dalilin da mista Peterside ya bayar ya shafi manufar musamman ta kasar Sin, ta tsara shirin raya kasa duk shekaru biyar-biyar, wanda ke da matsayi na wajibi tamkar doka. Ya ce, ci gaban da kasar Sin ta samu ya tabbatar da cewa, duk wata kasa za ta iya samun babban ci gaba ta hanyar tsayawa tsayin daka kan aiwatar da wasu nagartattun manufofi.
Tsokacin da Mista Peterside ya yi daidai ne. Saboda yin amfani da tsare-tsare na matsakaita, da na dogon lokaci wajen jagorantar aikin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, hanya ce mai muhimmanci ga jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin wajen gudanar da mulki a kasar. Tun daga shekarun 1950, kasar Sin ta fara tsarawa da aiwatar da shirye-shiryen raya kasa na shekaru biyar biyar, kuma yanzu muna cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5 na 14, wanda kasar Sin ta tsara. Hakika “Shirin shekaru biyar” na farko zuwa na biyar sun baiwa kasar Sin damar kafa wani cikakken tsarin masana’antu da na tattalin arziki. Kana “Shirin shekaru biyar” na shida zuwa na tara, sun ba jama’ar kasar Sin damar samun kyakkyawan yanayin rayuwa gaba daya. Ban da haka, a cikin wa’adin ” shirin shekaru biyar” na goma zuwa na goma sha biyu, jimillar tattalin arzikin kasar Sin ya daga zuwa matsayi na biyu a duniya. Sa’an nan, a cikin shekaru kusan 10 da suka wuce, wato a cikin wa’adin “shirin shekaru 5” na 13 da na 14, kasar Sin ta gina al’umma mai ingancin rayuwa, kuma karfin tattalin arzikinta, da na kimiyya da fasaha, sun kai wani sabon matsayi. Bisa alkaluman da kasar Sin ta fitar, an ce, a yayin “shirin shekaru biyar” na 14 da za a kawo karshensa a bana, ana sa ran karuwar tattalin arzikin kasar Sin za ta zarce dalar Amurka triliyan 4.9, adadin da ya zarta jimillar tattalin arzikin kasar da ke matsayi na uku a duniya a fannin karfin tattalin arziki.
- Sauye-sauyen Tinubu Suna Taimaka Wa Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya — Minista
- EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi
Me ya sa “Shirin shekaru biyar” na kasar Sin ya iya haifar da irin wadannan dimbin alfanu? Dalili shi ne wasu halayen musamman na shirin. Bisa tsokacin da mista Li Zhongjie, masanin ilimin tarihin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yi, “shirin shekaru biyar” na kasar Sin ya hada da halayen musamman na bin doka, da sanya moriyar jama’a a gaban komai, da daukar mataki bisa ainihin yanayin da ake ciki, da kokarin tabbatar da aiwatarwar manufofi.
A cikin wadannan halayen musamman, “sanya moriyar jama’a a gaban komai” na nufin: Na farko, yayin da ake tsara “Shirin shekaru 5”, dole ne a gudanar da bincike a tsanake a wurare daban-daban, da kuma sauraron ra’ayoyi daga kowane bangare. Misali, lokacin da aka tsara shirin “Shirin shekaru biyar” karo na 14, wasu shekaru biyar da suka gabata, baya ga gudanar da binciken, an kuma aiwatar da aikin neman ra’ayin jama’a kan layi, wato ta shafin yanar gizo na Intanet, a watan Agustan 2020, an kuma samu sama da shawarwari miliyan 1.018 daga masu amfani da yanar gizo. Na biyu, burin da ake neman cimmawa ta hanyar tsara “Shirin shekaru biyar” shi ne tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da kokarin biyan bukatun al’umma na fannoni daban daban. Saboda haka, duk wani “shirin shekaru 5” na kunshe da dimbin manufofin inganta rayuwar jama’a. Ma iya cewa, ana inganta zaman rayuwar jama’ar kasar Sin ne, ta hanyar aiwatar da “shirye-shiryen shekaru biyar” daya bayan daya.
Sa’an nan, “bin doka” yana nufin, yayin da aka tsara “shirin na shekaru biyar”, dole ne a bar dukkan jam’iyyun siyasa su yi tattaunawa mai zurfi a kansa, kana majalisar gudanarwar kasar Sin ta kula da aikin tsara shirin, kafin daga bisani majalissun dokokin kasar Sin su tantance shirin da kada kuri’a don zartar da shi, inda ake aiwatar da dukkan ayyukan bisa tsarin dimokuradiyya da kuma doka. Bugu da kari, kowace shekara, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta kan yi bitar ci gaba da aka samu, a kokarin aiwatar da “shirin na shekaru biyar” da aka tsara.
Ban da haka, bayan da aka tsara “shirin shekaru 5”, yana da muhimmanci a aiwatar da shi. A kasar Sin, bayan da aka gabatar da wani “shiri na shekaru 5”, dole ne a aiwatar da shi yadda ake bukata. Kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar za su tsara salon aiwatar da dukkan ayyuka, da raba su ga sassa da yankuna daban-daban, don a aiwatar da su a matakai daban daban. Bayan haka, hukumomi daban daban su kan gudanar da ayyukan sa ido a tsakiyar wa’adin shirin, kuma za a tantance ainihin sakamakon da aka samu bayan karewar shirin.
Ta wadannan halayen musamman, za a iya ganin abubuwan da za su tabbatar da aiwatar da shirin na raya kasa: Na farko, kokarin kare muhimman muradun jama’a, da tabbatar da yanke shawara ta wata hanya mai dacewa, kuma bisa tsarin dimokuradiyya. Na biyu, yin amfani da tsare-tsaren shari’a wajen tabbatar da ingancin shirin da aka tsara, da mai da shi karkashin sa ido da aka yi masa. Na uku, tun daga gwamnatin tsakiya zuwa kananan hukumomi, dole ne a aiwatar da shirin raya kasa a tsanake, domin tabbatar da cimma burin da aka sanya a gaba. A cikin wadannan abubuwa, ana iya ganin ruhin dimokuradiyya da bin doka da oda, da kuma yanayin aiki na mai da hankali, da nuna sanin ya kamata, wadanda suka kasance tushen ci gaban kasar Sin.
A cewar mista Peterside, ta hanyar koyi da fasahohin kasar Sin, Najeriya za ta iya cin gajiyar dimbin albarkatun kasa da take da su, don tabbatar da cikar burinta na raya tattalin arziki. Ni ma na yi imanin cewa, Najeriya za ta iya yin hakan, tare da samun biyan bukata. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp