Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan kasar Masar Hanafi Jabali a birnin Alkahira, fadar mulkin kasar Masar. Yayin ganawar tasu a jiya Laraba, Li ya ce Sin na fatan zurfafa mu’ammala da Masar, da gaggauta hadin gwiwarsu a bangaren raya tattalin arziki, da ciniki bisa jagorancin shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma tushen dandalin hadin kan Sin da kasashen Larabawa, da na Sin da kasashen Afirka.
Ya ce Sin na fatan kara habaka mu’ammala da Masar, don bangarori daban-daban za su kiyaye ka’idojin huldar kasa da kasa, da tsarin ciniki tsakanin mabambantan bangarori tare, ta yadda za a kara karfafa sha’anin shimfida zaman lafiya da bunkasar duniya.
- EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi
- Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda
A nasa bangare kuwa, Jabali ya ce Masar na fatan habaka hadin gwiwarta da Sin a bangaren ciniki, da zuba jari, da sabbin makamashi da sauransu, da kuma gaggauta hada hannu da mabambantan bangarori, don kiyeye tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban bisa tushen kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ta yadda za a tinkari kalubale tare.
Har ila yau a dai jiyan, Li ya gana da babban sakataren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa wato AL Ahmed Aboul Gheit a birnin na Alkahira. Inda ya ce Sin na fatan kara tuntubar AL a dandalolin MDD, da SCO da sauransu, don bayyana ra’ayinsu na bai daya, ta yadda za a gaggauta kafa tsarin daidaita harkokin duniya bisa adalci da gaskiya.
A nasa bangare, Gheit ya ce, AL na jinjinawa goyon baya da Sin ta dade tana baiwa kasashen Larabawa a dandalolin kasa da kasa, ciki har da MDD, yana kuma fatan kara hadin gwiwa da Sin, wajen taka rawarsu a fannin kiyaye manufar cudanyar mabambantan bangarori na duniya, da ciyar da zaman lafiya da bunkasar duniya gaba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp