Wasu ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai mummunan farmaki ga tawagar haɗin gwuiwar jami’an tsaro a ƙaramar hukumar Guma ta Jihar Binuwe, inda suka hallaka jami’an NSCDC biyu tare da jikkata wasu uku, yayin da jami’an tsaro guda uku suka ɓace.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NSCDC, Michael Ejelikwu, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho da wakilinmu, inda ya bayyana ASCI Adoli Simon da ASCI Ernest Tyolumun Ayilla a matsayin jami’an da suka rasa rayukansu a harin.
- Sarkin Musulmi Ya Nuna Baƙin Ciki Kan Kisan Kiyashi A Binuwe
- An Ceto Ɗalibai 20 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Binuwe
Wani jami’in tsaro da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana a ranar Alhamis, a kan hanyar Ukohol, yayin da tawagar ke gudanar da sintiri. A cewarsa, sun hango wani ƙauye da ke ci da wuta da makiyayan suka bankawa wuta, kuma suka yanke shawarar zuwa wajen domin tantance halin da ake ciki.
Sai dai, kafin su isa garin, an ce makiyayan sun kai musu farmakin ƙwantan ɓauna, inda suka harbe jami’an biyu nan take, suka kuma jikkata wasu da suka haɗa da Sufeto. Ochepo Benjamin daga rundunar ƴansanda da wani jami’in NSCDC da ba a bayyana sunansa ba.
Har yanzu dai wani Sufeto. Muhammed da wasu jami’an NSCDC biyu suna ba’a gansu ba, yayin da aka fara bincike da ceto domin gano inda suke. Rundunar ƴansandan jihar Binuwe dai, ta bakin PPRO, DSP Udeme Edet, ta ce ba ta da cikakken bayani kan harin a halin yanzu.
Tawagar da aka kai wa harin ta ƙunshi jami’an Police Mobile Force (13 PMF da 58 PMF), State Intelligence Services, Operation Zenda, CTU, NSCDC, da Binuwe Civil Protection Guards da kuma ƴan sa-kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp