ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 20, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Bai Taɓa Ba Ni Umarnin Yin Ƙarya Ko Cin Zarafin ’Yan Jarida Ba – Minista

by Sadiq
1 year ago
Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Tinubu bai taɓa ba shi umarnin yin ƙarya, ya tsare, ko ya gallaza wa kowane ɗan jarida ba, ko da kuwa suna suka gwamnatinsa.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) a Abuja.

  • UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
  • Akwai Bukatar Sin Da Masar Su Zurfafa Hadin Gwiwa Domin Kare Muradunsu

Ministan ya bayyana cewa, ko da wasu rahotanni daga kafafen yaɗa labarai ko furucin wasu mutane na zama masu zafi ko ɓatanci, Shugaba Tinubu bai taɓa ce masa ya ɗauki matakin ramawa ba.

ADVERTISEMENT

“Wasu lokutan kafafen labarai kan tayar da hankali,” in ji shi.

“Amma Shugaba Tinubu bai taɓa cewa na yi ƙarya ko na sauya gaskiya ko na kama masu laifi ba.”

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Ce A Shirye Yake Ya Sasanta Gwamna Yusuf

Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?

Ya ƙara da cewa, Tinubu na mutunta dimokuraɗiyya da doka.

Haka kuma, gwamnati ta san cewa ba za ta iya aiki yadda ya kamata ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.

Idris ya ce a baya, wasu jami’an gwamnati suna sukar gwamnati, amma shi kullum yana tattaunawa da ƙungiyar ’yan jarida da masu wallafa jaridu domin warware matsaloli cikin lumana.

“Idan muna yin daidai, ku yabe mu,” in ji shi.

“Idan kuma muna kuskure, ku faɗa mana cikin lumana domin mu inganta ayyukanmu.”

Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawar mu’amala da kafafen labarai kuma hakan zai ci gaba.

Ya roƙi ’yan jarida ka da su ɗauki wasu ƙananan matsaloli su yi wa gwamnati hukunci a kai gaba ɗaya.

Ya kuma bayyana wani babban ci gaba da aka samu a Nijeriya na dab da samuwa domin za a karɓi baƙuncin Cibiyar Wayar da Kan Jama’a kan Hanyoyin Yaɗa Labarai (MIL) a Jami’ar Open University da haɗin gwiwar UNESCO.

Wannan cibiyar za ta taimaka wajen ilimantar da mutane kan labaran ƙarya da yaɗa jita-jita.

“Da zarar an amince, mutane daga sassa daban-daban na duniya za su riƙa zuwa Nijeriya domin koyon dabarun kafafen yaɗa labarai,” in ji shi.

MASU ALAKA

Kwankwaso Ya Ce A Shirye Yake Ya Sasanta Gwamna Yusuf
Manyan Labarai

Kwankwaso Ya Ce A Shirye Yake Ya Sasanta Gwamna Yusuf

September 20, 2026
Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?
Wasanni

Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?

September 20, 2026
Trump Ya Hana CNN Da Wasu Kafofin Yaɗa Labarai Shiga Fadar White House
Kasashen Ketare

Trump Ya Hana CNN Da Wasu Kafofin Yaɗa Labarai Shiga Fadar White House

September 19, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda

Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu 'Yan Ta’adda

LABARAI MASU NASABA

Manyan Abubuwa 7 Da Za A Na Tuna Wa Da Tsohon Gwamnan Kogi Marigayi Ibro

Manyan Abubuwa 7 Da Za A Na Tuna Wa Da Tsohon Gwamnan Kogi Marigayi Ibro

September 20, 2026
Sin Ta Harba Tauraron Dan’adam Na Gwaji Da Ya Hade Ayyukan Sadarwa Da Tattara Bayanai Da Sarrafa Su

Sin Ta Harba Tauraron Dan’adam Na Gwaji Da Ya Hade Ayyukan Sadarwa Da Tattara Bayanai Da Sarrafa Su

September 20, 2026
Kano Pillars Ta Lallasa Doma United Da Ci 4-1 A Sani Abacha

Kano Pillars Ta Lallasa Doma United Da Ci 4-1 A Sani Abacha

September 20, 2026
Osimhen Ba Zai Buga Wa Nijeriya Wasannin Madagascar Da Guinea-Bissau Ba

Osimhen Ba Zai Buga Wa Nijeriya Wasannin Madagascar Da Guinea-Bissau Ba

September 20, 2026
An Bude Taron Masana’antun Kere-Kere Na Duniya Na Shekarar 2026 A Hefei Na Lardin Anhui

An Bude Taron Masana’antun Kere-Kere Na Duniya Na Shekarar 2026 A Hefei Na Lardin Anhui

September 20, 2026
Tinubu Ya Janye Shirin Halartar UNGA, Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya

Tinubu Ya Janye Shirin Halartar UNGA, Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya

September 20, 2026
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 9 A Sabbin Hare-Hare A Filato

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 9 A Sabbin Hare-Hare A Filato

September 20, 2026
Kwankwaso Ya Ce A Shirye Yake Ya Sasanta Gwamna Yusuf

Kwankwaso Ya Ce A Shirye Yake Ya Sasanta Gwamna Yusuf

September 20, 2026
NSCDC Ta Kama Mutane Biyar Kan Zargin Sayar Da Naman Mushen Shanu A Yobe

NSCDC Ta Kama Mutane Biyar Kan Zargin Sayar Da Naman Mushen Shanu A Yobe

September 20, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Radda Ya Ƙaddamar Da Shirin Tsaron Abinci Da Tallafawa Matasa A Katsina

September 20, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.