Ƙwallon da Chinwendu Ihezuo ta zura a minti na 89 ya isa ya kai babbar tawagar mata ta Nijeriya da akeyiwa lakabi da Super Falcons zuwa matakin Kwata Fainal na gasar cin kofin Afrika ta mata da hukumar CAF ke shiryawa ta shekarar 2025, Super Falcons ta doke kasar Botswana da ci 1-0 a wasan da suka buga yau Alhamis da karfe 8 na dare agogon Nijeriya a Casablanca.
A fafatawar da aka yi a filin wasa na Stade Larbi Zaouli, Ihezuo ce gwarzuwar wasan, sakamakon kwallo daya tilo da ta jefa a ragar kasar Botswana dake Kudancin Afirika, Nijeriya ta lallasa Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga, duk da cewa an tafi hutun rabin lokaci ba tareda jefa kwallo ko daya a raga ba, amma yan matan na Madugu sun nuna bajinta bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Asisat Oshoala da Toni Payne duk sun barar da damarmakin da suka samu kafin a tafi hutun rabin lokaci, hakazalika Balothany Johannes da Laone Moloi sun kai mugayen hare hare cikin kwarewa amma mai tsaron ragar Nijeriya Chiamaka Nnadozie ta ce ba yau ba.
Justin Madugu yayi canji uku a lokacin hutun rabin lokaci, inda ya gabatar da Christy Ucheibe, Esther Okoronkwo da Chinwendu Ihezuo don sauya salon wasan wanda kuma hakan ya bayar da sakamakon da ake bukata, wannan ce nasara ta biyu da Nijeriya ta samu a gasar yayinda har yanzu aka kasa zura mata kwallo a ragarta,Nijeriya ce ke kan gaba a rukunin B kuma ta tsallake zuwa zagayen gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp