Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce abu ne mai wahala matatun man fetur ɗin ƙasar nan mallakin gwamnati su ci gaba da aiki duk kuwa da maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ta yi ikirarin tana kashe wa wajen gyara su.
Da yake jawabi a lokacin da ƙungiyar shugabannin kamfanoni ta ƙasa da ƙasa ta kai masa ziyara a ofishinsa a jihar Legas, Ɗangote ya ce matatun man fetur na Fatakwal da Warri da kuma Kaduna ba lallai ne su dawo yin aiki ba saboda sun tsufa an daina yayinsu.
- Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Ababen More Rayuwa A Nijeriya
- Dangote Ya Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 820
Ya bayyana cewa a lokacin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, kamfaninsa ya sayi matatun man fetur ɗin amma bayan an samu canjin gwamnati ya mayar da su hannun gwamnati.
“Mun sayi matatun man fetur ɗin a watan Janairu na shekara ta 2007. Suna tace kashi 22 cikin ɗari na abin da ya kamata su tace na man fetur amma bayan an samu sauyin shugabanci sai aka ce mu mayar da su” in ji Ɗangote
A cewar Ɗangote, jami’an gwamnati ne a wancan lokacin suka gayawa marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua cewa kamfanin mai na NNPC zai iya ci gaba da kula da matatun.
Ɗangote Ya ƙara da cewa “A yau, bayan kashe sama da dalar Amurka biliyan 18 wajen gudanarwa tare da gyara matatun man har yanzu basa aiki. Kuma bana tunanin nan gaba za su iya ci gaba da aiki. Ƙoƙarin zamanantar da su kamar misalin zamanantar da tsohuwar motar da ta yi shekara 40 ne, ko an canja inji ba zai sa ta koma dai-dai da ta zamani ba”.
Alhaji Aliko Ɗangote ya ce ya yanke shawarar gina matatar man fetur ne mai fitar da ganga dubu ɗari shida da hamsin a rana bayan da marigayi Umaru Musa Yar’adua ya yanke shawarar ƙin siyar masa da matatun man fetur ɗin ƙasar nan.
Sabuwar matatar man fetur ta Ɗangote ana saran za ta saka Nijeriya ta rage dogaro da shigo da man fetur daga waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp