Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU), reshen jami’ar Abuja ta bayyana wa ‘yan Nijeriya cewa, yajin aiki zai ci gaba da gudana tun da har yanzu gwamnatin tarayya ta kasa daukan matakin da ya dace.
Shugaban kungiyar ASUU reshen jami’a Abuja, Dakta Kassim Umaru shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai jam kadan bayan taron kungiyar da ya gudana a harabar jami’ar Abuja da ke yankin Gwagwalada a ranar Talata.
Umaru ya kara da gwamnatin tarayya ita ce take da wuka da nama wajen kawo karshen wannan yajin aiki.
A cewarsa, kungiyar ta gabatar da matsalolinta kafin ta tunduma yajin aiki ga gwamnatin tarayya, amma sai ta yi watsi da su, inda sai da kungiyar ta zanta da majalisar zantarwa ta kasa har na tsawon makonni hudu kafin daukan wannan mataki.