• English
  • Business News
Sunday, August 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna

by Muhammad
3 weeks ago
in Labarai, Siyasa
0
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin da ke cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kwatanta matakan da tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka ɗauka dangane da cire ko dakatar da gwamna a lokacin da suke kan mulkinsu ba. Ta ce irin waɗannan rahotanni ba gaskiya ba ne, kuma an kirkire su ne saboda a tayar da ƙurar siyasa.

A wata sanarwa da Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Jumma’a, an bayyana zargin a matsayin ƙarya mai cike da soki-burutsu, tare da musanta jita-jitar cewa Shettima ya soki Shugaba Tinubu dangane da rikicin siyasa da ya faru a Jihar Ribas.

  • Wanda Ya Yi Gangancin Taba Takarar Shettima Ya Gayyato Wa APC Faɗuwa A 2027 – Aminu Boyi 
  • Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima

Sanarwar ta bayyana cewa jawaban da Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi a wajen ƙaddamar da littafin “OPL 245: The Inside Story of the $1.3 Billion Oil Block” wanda tsohon Antoni Janar na Tarayya, Mohammed Bello Adoke (SAN), ya rubuta, sun waiwaye ne kan tarihin baya saboda muhimmancin adana tarihin gwamnatoci, amma ba shi da alaƙa da sukar Shugaba Tinubu.

“Wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da mutane sun juyar da kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasa don cimma wata mummunar manufa,” cewar sanarwar. “Sun juya bayanin yadda gwamnatin Jonathan ta taɓa tunanin tsige Shettima daga matsayin gwamna a lokacin da rikicin Boko Haram ya yi tsanani.”

Sanarwar ta jaddada cewa Shettima yana bayar da labarin abubuwan da suka faru fiye da shekara goma da suka gabata, kuma ya yi haka don jinjina wa kyakkyawan halin Adoke a matsayin ma’aikacin gwamnati.

Labarai Masu Nasaba

Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

Etsu Nupe Ya Jaddada Buƙatar Sama Wa Sarakunan Gargajiya Gurbi A Tsarin Mulki

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yunƙurin da aka yi na haɗa waɗannan maganganun da abubuwan da suka faru a Jihar Ribas, musamman batun dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ayyana dokar ta-baci, fassara ce da aka yi ta ba daidai ba, ko kuma suka ne ga kundin tsarin mulkin ƙasa.

“Domin kaucewa ruɗani, Shugaba Tinubu bai cire Gwamna Fubara daga mukaminsa ba,” sanarwar ta jaddada. “Abin da aka aiwatar dokar dakatarwa ce, ba tsige wa ba. Wannan mataki da kuma ayyana dokar ta-baci an ɗauke su ne sakamakon rikicin siyasa mai tsanani da ya faru a Jihar Ribas a wancan lokacin.”

Sanarwar ta ce rikicin da ya faru a Ribas ya cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya gindaya na ɗaukar matakan gaggawa, bisa tanadin Sashe na 305(3)(c), wanda ke bayar da damar hakan idan an samu rashin zaman lafiya da tsaro a matsayin matakin da ya zama wajibi a yi amfani da shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 2027APCFadar Shugaban ƘasaShettimaTinubu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Jihohi 10 Sun Kinkimo Bashin Naira Biliyan 417 Duk Da Karin Samun Kudaden Shiga

Next Post

Amurka Ta Rage Wa’adin Bizar ‘Yan Nijeriya Zuwa Wata Uku

Related

Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12
Siyasa

Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

12 hours ago
Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto
Labarai

Etsu Nupe Ya Jaddada Buƙatar Sama Wa Sarakunan Gargajiya Gurbi A Tsarin Mulki

14 hours ago
Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto
Labarai

Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

17 hours ago
Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto
Labarai

Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto

17 hours ago
Ma’aikatan Jinya Sun Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu 
Da ɗumi-ɗuminsa

Ma’aikatan Jinya Sun Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu 

19 hours ago
Gwamna Fintiri Ya Karrama Kocin Super Falcons, Madugu Da Naira Miliyan 50
Labarai

Gwamna Fintiri Ya Karrama Kocin Super Falcons, Madugu Da Naira Miliyan 50

19 hours ago
Next Post
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Amurka Ta Rage Wa’adin Bizar 'Yan Nijeriya Zuwa Wata Uku

LABARAI MASU NASABA

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

August 3, 2025
Ban Yi Danasanin Shiga Harkar Fim Ba – Baba Ƙarami

Ban Yi Danasanin Shiga Harkar Fim Ba – Baba Ƙarami

August 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji

Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji

August 3, 2025
Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

August 3, 2025
Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

August 2, 2025
Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?

Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?

August 2, 2025
Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

Etsu Nupe Ya Jaddada Buƙatar Sama Wa Sarakunan Gargajiya Gurbi A Tsarin Mulki

August 2, 2025
Babban Bankin Sin Ya Yi Alkawarin Ba Da Goyon Baya Ga Kirkire-Kirkire Da Sayayya

Babban Bankin Sin Ya Yi Alkawarin Ba Da Goyon Baya Ga Kirkire-Kirkire Da Sayayya

August 2, 2025
Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya

Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya

August 2, 2025
Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

August 2, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.