Shugabannin kungiyar hadin gwiwa a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sun fara gudanar da gangami a yankunansu.
LEADERSHIP Sunday ta gano cewa shugabannin gamayyar, wato shugabanta na rikon kwarya na kasa, Sanata Dabid Mark, sakataren kasa, Rauf Aregbesola, sun koma jihohinsu, Benue da Osun domin neman goyon bayan al’ummarsu.
- Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa
- Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
A wani mataki na tabbatar da kafa sansanoninsu a yankunan nasu, an nakaltro cewa, an ba wa shugabannin gamayyar aikin kula da yadda dandalinsu zai kazance a yankunansu na siyasa.
A cewar wata majiya da ke kusa da aikin, Atiku ne zai jagoranci shiyyar Arewa maso Gabas; Dabid Mark ne zai jagoranci shiyyar Arewa ta tsakiya, yayin da El-Rufai zai jagoranci shiyyar Arewa maso Yamma.
A shiyyar kudancin kasar kuwa, Obi ne zai jagoranci shiyyar Kudu maso Gabas, yayin da Aregbesola zai jagoranci shiyyar Kudu maso Kudu da shiyyar Kudu maso Yamma.
Wata majiya ta tabbatar da cewa, a yayin da tsohon shugaban majalisar dattawan ya je Jihar Binuwai domin daurin auren jikarsa, “watakila zai yi ganawa da shugabanni da masu goyon bayan tafiyar a shiyyar.”
Aregbesola ya samu tarba daga magoya bayansa a lokacin da ya isa Jihar Legas jim kadan bayan kaddamar da jam’iyyar a Abuja.
A nasa bangaren, Atiku ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC na jihar Gombe a Abuja karkashin jagorancin tsohon minista kuma Sanata Idris Abdullahi a Abuja, a yammacin ranar Juma’a.
Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa shugabannin jam’iyyar “sun dawo ne domin tuntubar yankunansu tare da kafa hanyar kulla alaka da jama’a yadda ya kamata.”
“Yan Nijeriya sun riga sun yi taro, jama’ar da suka taru a wurin taron sun kasance ‘yan halal ne, abin da ke faruwa a jihar ke nan,” in ji shi.
Da yake tabbatar da shirin gangamin a yankunan, babban sakataren jam’iyyar ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce an ba shugabannin makwanni biyu daga nan sai su koma Abuja domin wani taron.
Ya ce, “Mambobinmu da shugabanninmu sun koma yankunan ne domin jan hankalin jama’a, tattara su, gami da tattaunawa da su.
“Karfinmu ya ta’allaka ga mutane ne ba bindiga ko ‘yan daba ba, jama’a ce karfinmu, bayan mun tattauna da su, nan da mako biyu za su dawo Abuja.
“Bayan haka ne za mu zauna, mu yi nazarin rahotanninsu da sauran abubuwan da za su biyo baya,” in ji shi.
Sauran shugabannin gamayyar kungiyoyin da aka gani suna hada kan al’ummomin jihohinsu a karshen mako, sun hada da tsohon ministan harkokin ‘yansanda, Maina Waziri a Jihar Yobe da kuma tsohon gwamnan Imo, Honarabul Emeka Ihedioha.
Ko shugabannin gamayyar za su kai bantensu?
An kaddamar da jam’iyyar ADC a ranar Larabar da ta gabata a Abuja a matsayin dandalin hadin gwiwa na sake fasalin siyasar Nijeriya gabanin babban zabe na 2027.
Ga dukkan alamu bullowar ADC ta sake farfado da ‘yan adawa yayin da tsofaffin manyan jam’iyyun adawa, PDP da Labour Party, suka shiga cikin rigingimun shugabanci.
Kiraye-kirayen da aka yi a taron na ranar Laraba ya nuna yadda yunkurin fitar da Shugaba Bola Tinubu daga ofishinsa ta hanyar dimokuradiyya.
Fitattun ‘yan siyasar adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Anambra Peter Obi ne suka halarci bukin kaddamar da jam’iyyar a Abuja.
Duk da su biyun daya ya zo na biyu daya na uku a zaben shugaban kasa da ya gabata wanda Tinubu ya lashe da kuri’u marasa rinjaye.
Sauran jiga-jigan siyasa a wurin taron sun hada da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, Sanata Dino Melaye, tsohon ministan matasa da wasanni Solomon Dalung, mawallafin kuma jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, tsohon gwamnan Jihar Benue, Gabriel Suswam, tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, Sanata Ireti Kingibe ta jam’iyyar Labour, da tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai Ememe.
Suna fatan sake kafa sabuwar jam’iyyar adawa irn ta 2013 wacce ta haifar da jam’iyyar APC da ta yi ikirarin samun mulki a shekarar 2015.
Yayin da jam’iyyar APC mai mulki, da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da tsohon dan takarar shugaban kasa na ADC, Dumebi Kachikwu suka yi watsi da jam’iyyar ADC da cewa ba ta da wata kima da za ta iya tsige Tinubu, shugaban riko na jam’iyyar, Sanata Dabid Mark, ya jaddada cewa jam’iyyar ta dukufa wajen ganin ta kubutar da kasar nan daga gwamnatin APC.
LEADERSHIP Sunday ta bayar da rahoto na musamman cewa an ba wa shugabannin gamayyar aikin kula da yadda za a fadada dandalin a yankunansu na siyasa a wani mataki na tabbatar da kafa sansanoninsu.
Yawancin shugabannin sun ziyarci jihohinsu. Magoya bayansa sun tarbi Aregbesola a Legas ranar Juma’a, inda suka nufi jiharsa, Osun. An kuma bayyana cewa Mark ya ziyarci jiharsa ta Benue jim kadan bayan kaddamar da bikin.
Duk da haka, ana yin tambayoyi game da yadda gamayyar za ta iya bai wa jam’iyyar APC tarnaki gabanin 2027. Wannan ya hada da kiraye-kirayen kasa da gogewar da manyan shugabannin kungiyar ke da shi.
Yayin da wasu manazarta ke amincewa da sunayen shugabannin gamayyar, za a gwada tasirinsu, musamman a jihohinsu da yankunansu, a yayin gudanar da zaben.
Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya shahara ba wai a jiharsa kadai ba, har ma a Nijeriya, kasancewar ya yi takarar shugabancin kasar fiye da kowane dan takara a tarihin siyasar kasar: tun a shekarar 1993 ya sanya idonsa kan kujerar koli.
Yayin da ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2003, ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a kusan kowane zagayen zabe.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 1999 da 2023 bai samu sauki ba a jiharsa ta Adamawa kwanan nan. Da alama alakar Atiku da gwamnan jiharsa, Umar Fintiri, ta yi tsami a kwanan baya.
Wani abin mamaki shi ne gwamnan bai fito fili ya nuna alaka da Atiku ba tun lokacin da aka fara yunkurin hadakar. A maimakon haka, Jibrilla Bindow wanda ya gaji Fintiri ya kara fitowa fili yana mai kusanci da Atiku, wanda hakan ke kara rura wutar rade-radin da ake yi na dawowar tsohon gwamnan kan karagar mulki a jihar.
Shaharar da Atiku ke da ita fiye da ta yankinsa abu ne sananne. Ya samu sama da kuri’u miliyan shida daga arewaci da kudancin kasar nan a zaben 2023 domin ya zo na biyu. Amma Tinubu, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a karon farko, ya lashe zaben da kuri’u sama da miliyan takwas.
Karfin Atiku na tattara kuri’u a jiharsa da kuma Arewa maso Gabas a jam’iyyar ADC zai yi daidai da na mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima wanda ya fito daga Jihar Borno a arewa maso gabas, da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, wanda ke jagorantar jam’iyyar APC a Jihar Adamawa.
Dabid Mark
Birgediya Janar (mai ritaya) a rundunar sojin Nijeriya ya yi gwamnan mulkin soja na Jihar Neja daga 1984 zuwa 1986. Ya zama Sanata na tsawon shekaru 20 tsakanin 1999 zuwa 2019. Ya zama shugaban majalisar dattawa mafi dadewa a kan karagar mulki, inda ya shugabanci majalisar na tsawon shekaru takwas ba tare da tsangwama ba tsakanin 2007 zuwa 2015.
Sai dai a baya Mark ya sha fafutukar ganin ya lashe zaben ‘yan majalisar dattawa wanda hakan ya sa wasu ke takun-saka da koken na sa a Jihar Benuwe. Amma bayan ya shafe shekaru takwas yana shugabancin majalisar dattawa, Mark da radin kansa ya ajiye mukaminsa na wakilin gundumarsa ta majalisar dattawa a jiharsa.
Aregbesola
Sabon sakataren jam’iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan Jihar Osun ne. Ya kuma rike ministan harkokin cikin gida a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari. Duk da cewa ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas, amma fafatawar da ya yi da wanda ya gaje shi, wanda yanzu ministan tattalin arzikin kasar nan, Gboyega Oyetola, ya sa ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta APC. Oyetola ya zama shugaban ma’aikata na Aregbesola tsawon shekaru takwas, amma ba shi ne wanda ya fi son tsayawa takarar gwamna a jihar ba.
Sai dai magoya bayansa, Omoluabi Progressibes, sun ce fitowar shugaban nasu a matsayin sakataren rikon kwarya na jam’iyyar ADC na kasa zai kara musu dama gabanin zaben gwamna a Jihar Osun a 2026.
Magoya bayan, a safiyar ranar Laraba, sun yi dafifi a harabar ofishinsu da ke jihar, suna rera waka da raye-raye ta murnar nadin sabon shugaban nasu.
Shugaban kungiyar Omoluabi Progressibes, Alhaji Isa Azeez, ya taya al’ummar Jihar Osun musamman ma Nijeriya murna kan sabon matsayin da Aregbesola ya samu, inda ya bayyana cewa an samu hazikin dan nasu wanda ya cancanci zama a sahun gaba.
Ya zuwa yanzu dai Aregbesola ya kasance wani abu a zaben da ya cire magajinsa wanda yanzu haka shi ne minista Oyetola daga mukaminsa.
Duk da cewa jigo ne a jam’iyyar APC, yanzu sakataren ADC na kasa ya goyi bayan dan takarar Sanata Ademola Adeleke, dan takarar PDP.
Sai dai Adeleke ya nisanta kansa daga kungiyar kawancen. Watakila aikin Aregbesola zai zama mafi wahala domin ya tallata sabuwar jam’iyyar a jiha da yankin Kudu maso Yamma inda shugaba Tinubu ya fito.
Amaechi
Tsohon gwamnan Jihar Ribas kuma ministan sufuri ya yi ta tofa albarkacin bakinsa game da kafa kungiyar. Amaechi wanda ya zo na biyu a gaban Tinubu a zaben fid da gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC 2023, tun daga lokacin ya nisanta kansa daga APC.
Sai dai a Jihar Ribas tsohon gwamnan ya sha gwagwarmayar kwace tsohuwar jam’iyyarsa ko da yana minista a gwamnatin Buhari.
Wanda ya gaji Amaechi a 2015 kuma ministan Babban Birnin Tarayya na yanzu, Nyesom Wike ya kwace jam’iyyar APC daga hannun tsohuwar minista a jihar. Wike, a matsayin gwamna, ya tabbatar da APC ba ta samu kuri’u a jihar ba, wanda hakan ya sa magoya bayan Amaechi suka sauya sheka.
Duk da haka, Amaechi ya yi imanin cewa har yanzu zai iya yin tasiri a jihar. Bayan sake haduwa da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar, zai yi sha’awar ganin yadda suka taka rawar gani a 2027.
Lamido
Lamido ya zama dan majalisar wakilai a jamhuriya ta biyu, sakataren jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) na kasa, kuma gwamnan jihar Jigawa na tsawon shekaru takwas tsakanin 2007 zuwa 2015.
Tsohon Ministan Harkokin Waje, Lamido ya zama kamar wani Sarki a Jihar Jigawa. Sai dai tun bayan da ya bar mulki a shekarar 2015 yake ta faman ci gaba da rike madafun ikon jihar da jam’iyyarsa ta PDP.
Dan gidan siyasar Aminu Kano, wanda shi ne uban jam’iyyar PDP, da kungiyar Muhammadu Buhari ta kifar da shi a shekarar 2015, har yanzu bai gama farfado da karfin siyasarsa a Arewa ba.
Lamarin da ya kara ta’azzara shi ne sakamakon zargin cin hanci da rashawa da gwamnati ke yi masa da ‘ya’yansa ta hannun hukumar ta EFCC.
Sai dai ya ce ba zai yi murabus daga jam’iyyar PDP ba duk da cewa yana goyon bayan ADC. Gabanin 2027, za a sake gwada tasirin siyasarsa a Jihar Jigawa da kuma yankin Arewa maso Yamma.
El-Rufai
Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, da ya nemi zama minista a gwamnatin Tinubu wanda a yanzu kuma yake neman ganin an kawar shi bayan majalisar dattawa ta dakatar da nadinsa na minista.
Yaron Buhari ne, kuma jigo a kungiyar hadakar jam’iyyar, ya yi gwamnan Kaduna na tsawon shekaru takwas bayan ya rike mukamin ministan Babban Birnin Tarayya.
Sai dai rashin jituwar da ke tsakaninsa da magajinsa, Sanata Uba Sani, wanda ya haifar da zargin cin hanci da rashawa da gwamnatin jihar ke yi masa, ya sanya El-Rufai cikin fafutukar ganin ya ci gaba da kasancewa a fagen siyasar jihar.
Tasirin da zai iya yi a jihar kafin shekarar 2027 zai zama abin ban sha’awa.
Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023 ya ba da mamaki a zaben da ya gabata. Karfinsa na samun sama da kuri’u miliyan shida kimanin shekaru biyu da suka wuce ya sanya shi a kan wani mataki karfi. Takararsa a 2023 ya ba wa ‘yan siyasa masu fafutuka damar lashe zabukan gwamnoni da na majalisun tarayya da na jihohi a fadin kasar nan.
Karfinsa na samun nasara a Legas, tushen siyasar Tinubu, ya ba da haske, kamar yadda ya shiga cikin jihohin tsakiya. Yana da iko a shiyyar Kudu maso Gabas da sauran yankuna na Kudu. Ya yi kira da babbar murya ga matasa da kuma wayar da kan jama’a a fadin yankuna.
Sai dai wasu na ganin cewa zaben Anambra da za a yi a watan Nuwamba zai zama ma’auni na farin jininsa a jihar da kuma yankin.
Aminu Tambuwal
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, wanda a yanzu Sanata ne ya kasa samar da wanda zai gaje shi a Jihar. Hasali ma, da kyar ya sake lashe zabensa a matsayin gwamna, wanda hakan ya nuna karara cewa ya rasa goyon bayan jama’a duk da kasancewarsa shugaban kungiyar gwamnonin PDP a lokacin.
Dan takarar shugaban kasa har sau biyu wanda Atiku ya sha kaye har sau biyu, abin jira a gani shi ne ko zai iya komawa jihar da ta koma karkashin jam’iyyar APC a karkashin tsohon aminin sa kuma mai taimaka masa, Sanata Aliyu Wammako.
Babangida Aliyu
Tsohon gwamnan Jihar Neja ya samu girma a lokacin da yake rike da madafun iko. Ya kasance shugaban jiga-jigan kungiyar gwamnonin jihohin Arewa kuma jigo a jam’iyyar PDP. Sai dai kamar yadda Tambuwal ya kasa kai wa PDP jiharsa bayan ya bar mulki. Tun daga wannan lokacin ya samu karancin martaba. Ko wannan sabuwar jam’iyyar za ta zaburar da shi wajen ganin ya tsaya tsayin daka a cikin makonni da watanni masu zuwa?.
Oyegun
Mutane da yawa sun yi mamakin ganin tsohon gwamnan Jihar Edo kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Odigie-Oyegun, a sansanin hadakar. Tabbas tun bayan ficewarsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC, ya ci gaba da nuna halin ko-in-kula. Tsohon babban sakatare ne da tsarin da ya dace da tsarin siyasa. Duk da haka, ba za a iya watsi da dimbin kwarewarsa ba.
Sauran ‘yan kungiyar da za a yi la’akari da abubuwan da suka shafi tasirinsu a jihohinsu da yankunansu, sun hada da tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami; tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; tsohon gwamna kuma mataimakin kakakin majalisa, Hon Emeka Ihedioha; tsohon ministan harkokin waje, Tom Ikimi; da tsohuwar shugabar mata ta PDP kuma minista, Josephine Anenih da sauransu.
Martani
A halin da ake ciki kuma, Chibuike Amaechi ya bayyana cewa zaben 2027 ba zai kasance kamar na baya ba, yana mai bayyana cewa ba za a bari a yi magudi da amfani da ‘yan daba ba.
Ya kara da cewa ba daidai ba ne a dauka cewa shugabannin kungiyar ba su da farin jini a jihohinsu, yana mai cewa yana da yakinin cewa yawancin shugabannin za su kawo jihohinsu.
“Wa ya gaya muku cewa ba mu da farin jini a jihohinmu, mu gwamnoni ne, sanatoci da jama’a suka zaba kuma muka hidimta musu, suna farin ciki da mu.
“Ku duba, zabe mai zuwa ba zai kasance kamar yadda aka saba ba, za a gudanar zabukan ne tsakanin jama’a da wasu ‘yan tsiraru kuma ina da tabbacin jama’a a shirye suke su kawo sauyi na gaskiya, ku jira ku gani.
“Ba za mu gaya muku dabarunmu ba, ‘yan Nijeriya nawa ne ke farin ciki da wannan gwamnati, nawa kuke samu kuma me kuke amfana da shi, ‘yan uwanku fa, suna farin ciki,” wannan ita ce tambayar da ya yi.
A nata bangaren, jam’iyyar ADC ta dage cewa ‘yan Nijeriya ba za su yi la’akari da sabbin shugabannin da suka gabata ba, ta kara da cewa abin da zai zo nan gaba ya wuce haka.
Kakakin gamayyar kungiyoyin ADC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar APC da fadar shugaban kasa za su yi mamakin irin nasarorin da jam’iyyar ta samu.
”Mun mayar da hankali kan abin da ya dace. Masu nishadantar da jama’a su ci gaba da munanan kalamai da ayyukansu, ” in ji shi.
A martaninsa, Sanata Abubakar Girei ya ce ‘yan Nijeriya ba za su amince da shugabannin gamayyar ba.
Sanata Girei, jigo a jam’iyyar APC, wanda ya wakilci mazabar Adamawa ta tsakiya a Jihar Adamawa daga 1999 zuwa 2003, ya ce shugabannin gamayyar sun fada cikin tarko.
“Idan aka yi la’akari da kasancewar mambobin kungiyar, a bayyane yake cewa su gungun mutane ne saboda dalilai daban-daban; yayin da wasu ke jin dadi saboda Shugaba Tinubu bai yi musu daidai ba, wasu kuma saboda dalilai na kashin kansu na son zama Shugaban kasa ta kowane hali.
“Da yawa daga cikin mutanen da ke kan gaba a wannan kawancen na neman sauyi, su ne wadanda suka ruguza Nijeriya, wadannan ba sabbin shiga siyasa ba ne, gogaggun ’yan wasan kwaikwayo ne da suka shafe shekaru da dama suna amfani da tsarin, da wawure baitulmali.
Me ya sa ‘yan Nijeriya za su amince da su don wani canji mai ma’ana? Ba za ku iya zama wani bangare na wadanda suka lalata tsarin ba, kuma yanzu kuna so ku yi ikirarin cewa ku waliyyi ne. Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana gyara kura-kuran da jama’a suka haifar,” in ji Girei.
Ya kamata APC ta yi hattara, Moniedafe ya yi gargadi
Da aka tambayi tsohon shugaban jam’iyyar ACN a Abuja, Sunny Moniedafe game da makomar sabuwar jam’iyyar da kuma karfin shugabanninta, ya ce dole ne APC ta yi taka-tsan-tsan da bullowar jam’iyyar ADC.
Jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce, “Har yanzu ina nan a jam’iyyar APC amma ina so in gargadi jami’an jam’iyyata da su yi taka-tsan-tsan, sai dai idan har suna da wata manufa ta daban, wato yin magudi, to za su fice daga Billa a 2027.
“Ta yaya APC za ta kasance da kwarin gwiwa a lokacin da ‘yan Nijeriya ke fama da yunwa da fushi da wahala?
“Ban san sauran shiyyoyin Arewa guda biyu ba, amma ga Arewa maso Gabas, akwai bukatar a samu canji cikin gaggawa,” in ji shi.
A nasa bangaren, Shugaban Matasan Arewa mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da shugabanci nagari, Alhaji Saliu Magaji, ya ce jam’iyyar APC za ta yi babban kuskure wajen raina jiga-jigan ‘yan siyasar ADC.
Ya ce, “A siyasa, ba ka raina kowa, fiye da irin wadannan ‘yan siyasa da ake girmamawa, su masu dabara ne, APC za ta rage musu illa, ba za ka iya korar mutane irin su Dabid Mark, Sule Lamido, Peter Obi, Chibuike Amaechi, da sauransu ba.
“Kar mu manta cewa wasu daga cikin shugabannin ADC ne suka kafa jam’iyyar PDP, don haka suna da kwarewa sosai, na ga jam’iyyar APC ta yi watsi da su a hankali, ina ba jam’iyya mai mulki shawara da ta hada kai tare da inganta ayyukanta yayin da take shirin tunkarar zabe mai tarnaki a 2027,” in ji shi.
Sai dai kuma tsohon dan takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa, Hon. Mohammed Saidu Etsu, ya yi imanin “babban hadin gwiwar” za ta ruguje.
Ya shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa, irin wannan mataki na iya zama kamar dabara, amma idan aka yi nazari sosai a kan wadanda abin ya shafa da kuma fagen siyasa, “wannan gamayyar ta yi rauni, ta rabu, kuma a karshe za ta ruguje.
Ya kara da cewa, “Bari mu fara da wasu daga cikin jiga-jigan wannan kungiyar, mu dauki tsohon Gwamna Nasir El-Rufai misali, zamansa a Jihar Kaduna ya haifar da matukar tashe-tashen hankula na addini da na kabilanci, musamman ma al’ummomin Kudancin Kaduna wadanda har yanzu suke ganin an mayar da su saniyar ware da kuma raunata su saboda manufofinsa, ga wanda ke neman goyon bayan kasa, wadannan tashe-tashen hankula da ba a warware su ba babban nauyi ne.
“Sai kuma Rotimi Amaechi, tsohon Ministan Sufuri, tun bayan da ya bar mulki, ya fice daga fagen siyasa, a Jihar Ribas, gidansa, tasirinsa a siyasa ya ragu matuka, musamman ganin yadda aka samu sabbin masu hada karfi da karfe irin su Honorabul Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda ya cike gibin da ya bari.
“Idan muka dubi Jihar Neja, inda na fito, lamarin siyasa ya kara fitowa fili, gwamna mai ci ya samu gagarumar nasara saboda a bayyane yake ta fuskar samar da ababen more rayuwa da inganta rayuwar matasa, farin jininsa ya kara karfafa goyon bayan jam’iyya mai mulki a fadin jihar, babu wani dan adawa mai gaskiya da ya ba da umarnin mutuntawa, biyayya, ko tsari don kalubalantar halin da ake ciki.
Bayan daidaikun mutane, ya ce babbar matsalar da ke tattare da kungiyar ita ce rashin hadin kan akida da karbuwarsa ga ‘yan kasa.
“Yawancin mambobinta suna da muradu mabambanta, buri na kashin kai, da kuma kishiyoyin da ba a warware su a baya ba. Samar da kawance don kayar da shugaban kasa mai ci ba tare da hadaddiyar manufa ba ko kuma ingantacciyar manufa, wannan hanya ce ta gazawa.”
Sai dai ya ce gwamnatin Tinubu na iya samun kalubalenta, amma shugaban kasa ya kafe a tsarin jam’iyyar.
“Ya ci gaba da ba da umarnin biyayya a manyan yankuna kuma ya nuna gwanintar siyasa wajen kulla kawance, t
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp