Matakin da shugaban Amurka ya dauka na katse mafi yawan tallafin da Amurka ke bai wa kasashe, ka iya haddasa mutuwar fiye da mutum miliyan 14 nan da 2030, kamar yadda binciken mujallar kiwon lafiya ta Lancet ya nuna.
Kashi uku cikin hudu na wadanda ke cikin hatsarin mutuwar kananan yara ne, a cewar binciken.
- Dan Gidan Ancelloti Ya Zama Sabon Kocin Botafago FC
- Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da AmurkaÂ
Kasashe masu karamin karfi da masu matsakaicin samu ne kan gaba wajen fuskantar barazanar katse tallafin.
Ana kwatanta katse tallafin da annoba ko gagarumin yaki,” a cewar Dabide Rasella, wanda ke cikin wadanda suka wallafa rahoton.
A watan Maris Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ya ce an soke fiye da kashi 80 cikin 100 na duka shirye-shiryen hukumar bayar da agaji ta Amurka (USAID).
Shugaba Trump da abokansa sun ce sun gano cewa ana tafka almundahana da zamba a hukumar.
Rahoton na zuwa ne yayin da gomman shugabannin duniya ke taro a Birnin Sabeilla na kasar Sifaniya cikin makon nan domin tattauna batun katse tallafin, wanda ya fi kowane bayar da agaji a duniya.
Bayan nazarin bayanan alkaluman tallafin hukumar a kasashe 133 a duniya, binciken ya kiyasta cewa tallafin USAID ya rage mutuwar mutum miliyan 91 a kasashe masu tasowa tsakanin 2001 zuwa 2021.
Sun kuma yi amfani da wani kiyasi wajen hasashen yadda rage tallafin da kashi 83% adadin da gwamnatin Amurka ta sanar a farkon wannan shekara na iya shafar adadin masu mutuwa.
Rahoton ya ce katse tallafin zai haifar da mutuwar miliyan 14 nan da shekarar 2030.
Adadin ya kunshi yara fiye da miliyan 4.5 ‘yan kasa da shekara biyar, kwatankwacin mutuwar kananan yara 700,000 a kowace shekara.
Gwamnatin Trump karkashin sabuwar hukumar kula da kashe kudaden gwamnati, da a baya hamshakin attajirin nan Elon Musk ya jagoranta, ta kudiri aniyar rage kashe kudaden gwamnatin tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp