Majalisar Dattawa ta ce ba za ta dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba har sai ta karɓi kwafin hukuncin kotu, ta kuma yi nazarinsa kan shari’arta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.
An dakatar da Natasha a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida saboda rikicin da ya shiga tsakaninta da shugabancin majalisar kan sauya mata wurin zama da kuma zargin cin zarafi, wanda hakan ya sa aka janye albashinta da jami’an tsaronta, kuma aka hana ta shiga zauren majalisa.
- Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta
- Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba
Bayan haka, ta garzaya kotun tarayya a Abuja, inda alkalin kotun, Mai shari’a Binta Nyako, ta umarci majalisar ta dawo da ita, tana mai cewa dakatarwar ta yi yawa kuma ta saɓawa kundin tsarin mulki. Amma kotun ta same ta da laifin raini ga kotu saboda wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta kuma umarce ta da ta biya tarar Naira miliyan biyar da kuma bayar da hakuri a manyan jaridu biyu da shafinta na Facebook cikin kwanaki bakwai.
Majalisar Dattawa ta ce har yanzu ba ta samu cikakken hukuncin kotun ba, kuma ba za ta dauki wani mataki ba sai ta karanta, ta kuma fahimci abin da hukuncin ya ƙunsa.
Majalisar ta ce tana da ikon tsara dokokinta da yadda ake gudanar da harkokinta, kuma dole ne a bi dokokin majalisar kafin a iya dawo da Sanata Natasha.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp