An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17, ga Disamba, 1942, a garin Daura na Jihar Katsina, Nijeriya. Shi ne ɗa na 23 a cikin yaran Malam Harɗo Adamu, wani shugaba Fulani da ya fito daga garin Dumurkul da ke ƙaramar hukumar Mai’Adua ta jihar Katsina, da mahaifiyarsa Zulaihat.
Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari shi ne mutum na shida da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya a Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya rasu yana da shekaru 82 (2025 – 1942) a yammacin a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan bayan ya sha fama da doguwar rashin lafiya.
- Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari Ya Rasu A Landan
- Tinubu Ya Tabbatar da Rasuwar Buhari, Ya Tura Shettima Zuwa Landan
Ga wasu manyan abubuwa 10 da kowa zai so ya sani game da rayuwar Marigayi Buhari:
1. Hawa Shugabanci Karo Biyu – Soja Da Siyasa
Buhari ya shugabanci Nijeriya a matsayin shugaban mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, sannan kuma aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2015 zuwa 2023.
2. Ƙwararren Soja, Ɗan Yaƙin Basasa
Ya shiga soja a 1962, ya samu horo a Burtaniya, kuma ya yi yaki a lokacin yaƙin basasa, inda ya jagoranci bataliya da manyan hare-hare a yankin gabas.
3. Ƙaddamar Da Yaƙi Da Rashin Ɗa’a (WAI)
A mulkinsa na soja, Buhari ya ƙaddamar da shahararren shirin yaƙi da rashin ɗa’a, don ya gyara halayen jama’a da ƙarfafa kyawawan ɗabi’u da kishin ƙasa.
4. Mulki Tsauri A Shekarun 1980
Mulkinsa na soja ya ƙunshi dokoki masu tsauri da daure ’yan jarida da sallamar ma’aikata daj yanke hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi.
5. Shugabantar Kula Da Asusun PTF
A ƙarƙashin mulkin Janar Abacha, Buhari ya shugabanci PTF, inda aka yabawa ayyukansa na1 gaskiya da gina ababen more rayuwa.
6. Ya Yi Takara Huɗu, Ya Ci Zaɓe A Karo Na Ƙarshe
Buhari ya tsaya takara a 2003 da 2007 da 2011, amma sai a shekarar 2015 ya lashe zaɓe a matsayin shugaban ƙasa kuma ɗan jam’iyyar APC, inda ya kayar da Shugaba Goodluck Jonathan.
7. Ya Mayar Da Hankali Kan Yaƙi Da Rashawa Da Samar Da Tsaro
A mulkinsa na farar hula, ya mayar da hankali kan yaƙi da rashawa da yaƙi da Boko Haram da samar da shirye-shiryen tallafawa matasa kamar shirin N-Power.
8. Doguwar Jinya Ta Yi Tasiri A Mulkinsa
Ya sha barin ƙasa don neman lafiya, ciki har da watanni huɗu a 2017, lamarin da ya jawo damuwa da firgici kan yanayin lafiyarsa da tafiyar da mulki.
9. Ƙalubalen Zanga-Zangar #EndSARS
A 2020, gwamnatinsa ta fuskanci babbar zanga-zangar matasa kan cin zarafin ’yansanda (#EndSARS), wadda ta zama jigo a tarihin mulkinsa.
10. Miƙa Mulki Cikin Lumana Da Komawa Daura
A ranar 29 ga Mayu, 2023, ya miƙa mulki ga Shugaba Tinubu, sannan ya koma mahaifarsa garin Daura na jihar Katsina, bayan ya kammala aikin gwamnati na aƙaalla shekaru 50.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp