Jam’iyyar NNPP ta ce bata mance da karfin jam’iyyun PDP da APC ba amma tana gina shirye-shirye domin karawa da su.
tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Goodluck Jonathan kuma Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rufai Alkali, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a ranar Laraba a Legas.
- 2023: A Shirye Muke Mu Bude Kofar Kulla Kawance Da Sauran Jam’iyyu Kafin Zabe –NNPP
- Rikicin NNPP: Kwankwaso Ya Ci Amanarmu – Shekarau
Alkali, wanda ya taba zama tsohon sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, ya ce jam’iyyar NNPP zata ba da mamaki a fadin kasar nan a babban zaben 2023.
Ya ce irin shugabancin da jam’iyyar NNPP zata kawo a Nijeriya zai sha bamban da yadda sauran jam’iyyun siyasa suka bayar ko kuma suke bayarwa.
“Mun fito ne don rage ɓacin rai da fushi da ɗaci a cikin ƙasar nan.
“NNPP jam’iyya ce da ta kafu da nufin zata kawo ci gaban Nijeriya.
“Yanzu mun samu ‘yan takararmu a matakai daban-daban kuma muna shirye-shiryen tunkarar yakin neman zabe nan ba da dadewa ba.
“Hakika, ba mu manta da karfi da tasirin da PDP da APC za su iya yi ba. Jam’iyyarmu tana kan hanya, muna da karfi sosai. Muna kara karfi. Mun shirya.
Shugaban wanda ya ce ‘yan Nijeriya na bukatar canji na gaskiya, ya ce jam’iyyar NNPP a shirye ta ke ta zaburar da jama’a domin gudanar da zabe a 2023.
Alkali ya yi nuni da cewa, kasashe da dama da ba su da dimbin albarkatu kamar yadda Nijeriya ta samu damar yin amfani da abinda ake da su don gina kasa.
Ya ce, ya kamata Nijeriya ta kasance daya daga cikin manyan kasashen nahiyar Afirka.
“’Yan Nijeriya na da burin ganin Nijeriya ta zama kasa mai inganci, ganin cewa mu ne mafi yawan al’ummar bakaken fata a nahiyar.
“Har ila yau, akwai tunanin cewa bayan shekaru 22 na mulkin dimokuradiyya, ya kamata kasar ta girma cikin nasara.
“A ka’ida, ya kamata mu yi nisa fiye da inda muke yanzu. Tsaro da tattalin arzikin al’umar kasar na fuskantar matsin lamba. A cewar Alkali.