An tsaurara matakan tsaro a gidan tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari, da ke Daura kafin gudanar da jana’izarsa a ranar Talata.
Dakarun tsaro da suka haɗa da Sojoji, ‘Yansanda, da Hukumar DSS sun kafa sun tsare domin tabbatar da tsaro.
- Trump Ya Bai Wa Rasha Kwanaki 50 Ta Kawo Ƙarshen Yaƙinta Da Ukraine
- Na Yafe Wa Buhari Duk Abin Da Ya Min – Buba Galadima
Tun da misalin ƙarfe 8 na safe, jami’an tsaro suka rufe hanyoyin shiga gidan gaba ɗaya, yayin da waɗanda kawai aka amincewa ke shiga gidan.
An tsaurara tsaron ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin jana’izar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025, a wani asibiti da ke birnin Landan bayan fama da rashin lafiya.
Ga hotuna a ƙasa: