Wani makisancin gwamna Nyesom Ezenwo Wike kuma babban darakta janar na Kungiyar Wike Solidarity Movement (WSM), Dr Prince Sudor Nwiyor, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC a jihar Ribas.
Nwiyor, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar malaman makarantu (ASUP) a Kenule Saro-Wiwa Polytechnic, Bori, ya samu tarba a jam’iyyar APC ta hannun dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Fasto Tonye Cole.
- Rikicin PDP: Bayan Ganawar Tinubu Da Wike A Landan, Ba Shiri Atiku Ya Garzaya Birtaniya
- PDP Ta Shiga Fargaba Bayan Wike Ya Yi Ganawar Sirri Da Tinubu
Da yake jawabi yayin bikin karbar, Nwiyor, wanda ya kasance mataimakin daraktan kamfen da yada angizon takarar Wike a zaben 2019, ya ce ya yi fice daga jam’iyyar PDP tun ranar 12 ga watan Agusta, 2022.
Ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP ne sakamakon rashin tsarin jam’iyyar da kuma rashin kawo ci gaba a fadin jihar a karkashin gwamnatin Wike.
Nwiyor ya godewa Dimkpa bisa kan ya taimaka masa ya koma APC, ya kara da cewa ya yanke shawarar shiga jam’iyyar ne sakamakon kyawawan halaye na dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da mataimakinsa, Dokta Innocent Barikor.
Ya bayyana cewa ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar sun gaji kuma sun fusata, kuma a shirye suke su bar jam’iyyar saboda kabilancin shugabanci a jam’iyyar a wannan gwamnati.
Babban Malamin ya yi ikirarin cewa nan da kwanaki masu zuwa zai ruguje dukkan tsarin kungiyar Wike Solidarity Movement (WSM) a fadin jihar zuwa jam’iyyar APC.