Shugaban Jamiyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufai Alkali, ya karyata jita-jitar da ake yada wa kan cewa, NNPP zata rusa shirinta don ta hade da dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC mai mulki, Bola Ahmad Tinubu, ba.
Alkali wanda ya karyata hakan a hirarsa da manema labarai a jihar Legas, ya mayar da martanin ne kan jita-jitar da ake yadawa ta cewa magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jamiyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, na kan tattaunawa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, don hade wa a inuwa daya.
- 2023: APC Da PDP Sun Riga Sun Yi Karfi Ita Kuma Jam’iyyar NNPP Na Kara Karfi –Rufa’i Alkali
- 2023: A Shirye Muke Mu Bude Kofar Kulla Kawance Da Sauran Jam’iyyu Kafin Zabe –NNPP
Al’kali ya bayyana cewa, jamiyyar bata shirya hade wa da kowa ba saboda Jamiyya ce mai cin gashin kanta da aka yi wa rijista.
Shugaban ya ce, an rufe duk wata dama ta hadewa a tsakanin jamiyyu, inda ya buga misali da dokoki da ka’idojin zaben 2023 da INEC ta fitar.
Da yake yin tsokaci a kan ficewar Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya yi daga cikin NNPP, Alkali ya ce, jamiyyar ta girmama hukuncin da ya dauka domin ba za mu yarda mu saka jamiyyarmu a cikin wani rikici ba.
Shugaban ya nananta cewa, NNPP ce kawai zan ta zamewa APC da PDP karfen kafa a zaben 2023, inda ya ce, a saboda haka, maganar hadewa da Bola ba za ta yuwu ba.