A wani mataki na sauƙaƙa samun damar yin biza na Birtaniya ga matafiya daga Arewacin Nijeriya, kamfanin VFS Global tare da haɗin gwiwar Hukumar Biza da Shige da Fice ta Birtaniya (UKVI) sun kaddamar da sabuwar Cibiyar Aikace-aikacen biza ta Musamman a Kano.
An buɗe cibiyar ne a Bristol Palace Hotel, lamba 54–56 titin Guda Abdullahi, inda za ta bai wa mazauna Kano da sauran yankunan Arewa damar gabatar da buƙatun biza da yin rijista cikin sauƙi, musamman kafin lokacin tafiye-tafiyen bazara da ke tunkarowa.
- Kasar Sin Ta Ba Baki Masu Yawon Bude Ido Dake Cikin Jiragen Ruwa Na Nishadi Izinin Shiga Kasar Ba Tare Da Visa Ba
- Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19
Hajiya Gill Lever, wadda ke matsayin Chargée d’Affaires a ofishin jakadancin Birtaniya da ke Abuja, ta bayyana jin daɗinta game da faɗaɗa ayyukan bada biza a Nijeriya.
“Ina farin cikin tabbatar da ci gaba da faɗaɗa ayyukan bada biza na Birtaniya a faɗin Nijeriya, da kaddamar da sabuwar Cibiyar Aikace-aikace ta Musamman ta VFS a Kano,” in ji ta. “Kano da sauran Arewacin Nijeriya na da matuƙar muhimmanci a dangantakar Birtaniya da Nijeriya. Sabuwar cibiyar za ta taimaka wajen sauƙaƙa wa mutane samun ingantaccen sabis na biza a kusa da inda suke.”
Ta kuma bayyana cewa Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke da yawan masu ziyartar Birtaniya daga nahiyar Afirka, inda take cikin ƙasashe huɗu mafi yawan masu nema, kuma tana da kusan kashi 6 cikin 100 na adadin aikace-aikacen biza a duniya.
Wannan cibiyar da aka buɗe a Kano ita ce ta uku da VFS Global ta kaddamar a cikin ‘yan watannin baya a Nijeriya, bayan buɗe makamantansu a Enugu da Port Harcourt. Cibiyoyin na ƙara wa waɗanda ke Abuja da Legas (Ikeja da Victoria Island), waɗanda ke aiki tun daga Nuwamba 2024.
Mista Alok Singhal, shugaban yankin hamadar nahiyar Afirka na VFS Global, ya jaddada aniyar kamfanin na kawo sauƙi ga abokan cinikinsu.
“Muna farin ciki da ƙara yawan wuraren da za a iya samun sabis na biza cikin sauƙi ga ‘yan Nijeriya, musamman da buɗe sabuwar cibiyar mu ta Musamman a Kano,” in ji shi. “Yayin da buƙatar tafiya zuwa Birtaniya ke ƙaruwa, burinmu shi ne mu samar da irin ingantaccen sabis, sauƙi da jin daɗi da muke bayarwa a Abuja da Legas a nan Kano.”
Sabuwar cibiyar da ke Kano na bayar da sabis na musamman da suka haɗa da taimako wajen lodin takardu, sanarwa kai-tsaye kan matsayin aikace-aikace, da isar da takardu ta hanyar sakonni. Haka kuma, abokan ciniki za su iya amfani da sabis ɗin “Ajiye Fasfo ɗina Bayan sa hannu”, wanda ke ba su damar ci gaba da amfani da fasfo ɗinsu bayan rijistar, sannan su miƙa shi daga baya idan an yanke hukunci.
Kamfanin VFS Global wanda ke aiki da ‘UK Visas and Immigration’ tun shekarar 2003, ya soma bayar da sabis a ƙasashe 58. A shekarar 2023, an sake ba su kwangilar bayar da sabis a ƙasashe 142, alamar yarda da ƙwarewarsu a fannin.
Ga mazauna Kano da sauran yankunan Arewacin Nijeriya, wannan sabuwar cibiyar na nufin ƙarin sauƙi, jin daɗi da saurin aiki – wanda zai ƙarfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Birtaniya a fannonin kasuwanci, yawon buɗe ido, ilimi da musayar al’adu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp