Ƙungiyar haɗin kan al’ummar Buzaye mazauna Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ali Muhammad Agadez, ta miƙa saƙon ta’aziyya ga Gwamnatin Nijeriya da iyalan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, bisa rasuwarsa da aka sanar a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.
A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan wani taron Ƙungiyar a Kaduna a ranar Talata, Alhaji Ali Agadez ya bayyana Buhari a matsayin gwarzon shugaba mai kishin ci gaban nahiyar Afrika, wanda rasuwarsa ta bar babban giɓi ga Nijeriya da ma ƙasashen yankin.
- Tawagar Likitoci Ta Sin Ta Ba Da Horon Fasahar Likitancin Gargajiya Ta Sin A Nijar
- Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
“Mun yi babban rashi a wannan lokaci. Saboda haka muke miƙa wannan gaisuwar ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa, ya kuma sa aljanna ta zama makomarsa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, ƙungiyar na jajanta wa ɗaukacin ‘yan Nijeriya da iyalan Buhari, yana mai roƙon al’umma da su ci gaba da yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya, fahimta da bunƙasa tattalin arziƙi a tsakanin al’ummomin yankin.
Ali Agadez ya kammala da cewa Buhari ya kafa tarihi mai ɗorewa a matsayin shugaban da ya yi ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro da yaƙi da cin hanci a Nijeriya, tare da barin ƙaddara mai nauyi da za a ci gaba da nazari a kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp