Sojojin Nijeriya sun cafke mambobi biyu na Ƙungiyar Ma’aikatan Hanyoyin Mota ta Ƙasa (NURTW) a Jihar Borno bisa zargin karɓar kaya daga masu tayar da ƙayar baya na IPOB.
Haka kuma, an kama wani da ake zargi da karɓar haraji a madadin Ƙungiyar ‘Yan Asalin Biafra (IPOB) da (ESN) a Jihar Anambra, inda aka kwato Naira miliyan 1.5 a hannunsa.
- Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
- Dokar Zaman Gida Ta IPOB Da Matakin Gwamnatin Tarayya A Sikeli
Shugaban Sashen yaɗa Labaran rundunar Sojin Nijeriya, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake bayani kan nasarorin da sojoji ke samu a fagen fama.
A yankin Arewa maso Gabas, an kama mutane 11 da ake zargi da haɗin gwuiwa da ‘yan ta’adda, tare da ceto mutanen da aka sace guda bakwai.
A jihar Yobe, Sojojin sun cafke wani ɗan shekara 65 da ke sayar da kayayyakin amfani ga ‘yan ta’adda. Haka kuma, Sojojin sun samu kakin Sojoji, da batir, da bindigu, da kuma kuɗi har Naira 17,150. A Bama, mata hudu da yara 12 daga ciki iyalan ‘yan ta’adda sun miƙa wuya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp