Wani dalibin Jami’ar Tarayya ta Dutsinma dake jihar Katsina dan shekara 24, Najeeb Shehu Umar ya hallaka kishiyar Mahaifiyarsa, Hajiya Hasiya Galadima yar shekara 65 kuma tsohuwar ma’aikaciyar Gwamnatin jihar har Lahira.
Najeeb wanda a yanzu ya ke a kan zangon karatunsa na uku a jami’ar ya aikata kisan ne a gidansu da ke jerin rukunin gidaje na Ambassadors Quarters da ke jihar Katsina.
An ruwaito cewa, a yayin hatsaniyar Najeeb ya maka wa mahaifinsa Shehu Umar Balele, karfe a kafa, inda mahaifin ya samu karaya wanda a yanzu ake yi masa magani a Asibitin kwararru na Kashi dake jihar.
Har ila yau, Najeeb an ce, yana yin ta’ammali da kayan maye, a wasu lokuta da dama, ya sha yin barazanar zai kashe Hajiya Hasiya bisa zargin da yake yiwa mariganyiyar na cewa ita ce silar da ta sa Mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa.
Babban Da a gun mahaifinsu, Mustapha Shehu Umar, wanda shi ma a gida daya yake zaune da iyayen na su ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce , dan uwansa ya sha yin barazanar kashe marigayiyar, amma mahaifinmu na dakatar da shi, inda yakara da cewa har ta kai ga an kai maganar gaban ‘yansanda.
Ya sanar da cewa, Najeeb ya shiga dakin marigayiyar Inda ya same ta, tana zaune sai ya ce, “nazo tunasar da ke kan maganar kashe ki da nace zan Yi” sai kawai ya maka mata wani karfe a kai har sau biyu, inda a nan take ta fadi.
Ya ce, makwabta ne suka yi gaggawar sanar da ‘yansanda, inda suka iso anguwar suka kama shi.