Domin cigaba da kin amicewa da takatarar musulmi da musulmi a cikin jam’iyyar APC, yanzu haka tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, hadi da wasu kiristoci na jam’iyyar APC sun bazama neman shawarorin wanda za su mara wa baya a yayin babban zaben 2023.
A cewar wata majiya, hadakar su na cigaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a kasar nan da wasu manyan ‘yan siyasa don duba wanene za su mara wa baya a cikin ‘yan takarar shugaban kasa da suka kunshi Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ko kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour Party.
Idan za ku iya tunawa dai, a kwanakin baya wadannan kusoshin sun gudanar da wani taron kungiyar kiristoci ‘yan arewa na jam’iyyar APC a Abuja, taron da ya samu wakilcin daga jihohin 19 na jihohin arewa da babban birnn tarayya inda suka amince suka cimma matsayar yin fatali da tikitin musulmi da musulmi a jam’iyyar APC.
Kazalika, Dogara da Babachir hadi da rakiyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba sun gana da tsohon shugaban kasa a zamanin mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa da ke Hilltop a Minna ta jihar Neja, kana sun kuma nausa suka gana da tsohon shugaban kasa a mulkin soji Janaral Abdusalami Abubakar.
Ganawar wacce ta gudana a ranar Litinin, makusantan ‘yan siyasan sun ce sun je Minna ne domin taya IBB murnar zagayowar ranar haihuwarsa inda ya cika shekara 81 a duniya, kuma dai sun nemi shawararsa kan matakin da ya dace su dauka dangane da tikitin musulmi da musulmi a jam’iyyar APC.