Jihar Kano zata karɓi baƙuncin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu GCFR a ranar Juma’a 18 ga Yuli, 2025, domin yin gaisuwar ta’aziyya ga gwamnatin jihar da al’ummar Kano, da kuma iyalan marigayi dattijon ƙasa, babban ɗan kasuwa kuma mai bayar da tallafi, Alhaji Aminu Dantata.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Alhamis.
- Gudummawar Sin Ga Tattaunawa Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai Da Dunkulewar Duniya
- Tinubu Zai Tarbi Gawar Buhari A Daura Don Yi Mata Jana’iza
Ziyarar na biyo bayan rasuwar mashahurin ɗan kasuwa da ya kafa tarihi ta hanyar yin hidima, da kyauta, da zuba jari da suka shafi rayuwar dubban ‘yan Nijeriya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana ziyarar a matsayin alamar haɗin kan ƙasa da girmamawa ga al’ummar Kano da kuma gadon marigayi Aminu Alasan Dantata.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su tarɓi shugaban ƙasar cikin mutunci da martaba, kamar yadda jihar Kano ta saba wajen girmama shugabanni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp