Sojojin Rundunar ta 6 ta Sojan Nijeriya, Sashen n 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun daƙile kai wani harin ta’addanci da aka shirya Taraba, bayan kama wasu mutane biyu da ake zargi da ta’addanci da kai hare-hare a wurare dabam-dabam a jihar.
Kakakin rundunar ta 6, Kyaftin Olubodunde Oni, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 17 ga Yuli, 2025.
- Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba
- Sojoji Sun Harbe Wani Ɗan Bindiga, Sun Ƙwato Makamai Bayan Artabu A Taraba
“Sojojin da ke sansanin FOB Wukari sun kama wani mai shekaru 45 mai suna Felix Myina, ɗan asalin karamar hukumar Ukum a jihar Benue.
“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin babban mamba ne a wata ƙungiyar gungun ‘yan fashi da garkuwa da mutane da ke aiki ƙarƙashin wani mai suna Mcianan, wanda aka fi sani da Yellow,” cewar Oni.
Ya ce wannan gungun ‘yan ta’addar suna daga cikin barazana ga matafiya da mazauna yankin Jootar–Wukari.
Sojojin sun kwace waya kirar Tecno daga hannun Myina a lokacin da aka kama shi.
A wani ci gaban kuma, Oni ya ce wasu sojojin sun kama wani da ake zargin mamba ne a kungiyar ISWAP mai suna Abubakar Yusuf, ɗan asalin jihar Borno da ke zaune a Gassol.
“An kama shi ne yayin da yake gudanar da wasu al’adu a kofar fadar Aku-Uka a Wukari, wuri da ake ganin ISWAP na shirin kai hari,” in ji Oni.
An ce yana ƙoƙarin amfani da aljanu don sauƙaƙa wa ‘yan ta’adda kai hari.
Kayan da aka kama shi da shi sun haɗa da kaza matacciya da ƙwai tara da suka lalace da ƙahon dabba da kwalbar da ke ɗauke da garin wani abu, da ƙananan naman daji.
Ana cigaba da bincike yayin da dukkansu ke tsare a hannun rundunar sojin ta 6.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp