Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Iliya Damagum, ya bayyana cewa har yanzu karfi da ikon jam’iyyar PDP yana nan bai samu tawaya ba bayan ficewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya fice daga jam’iyyar kwanaki biyu da suka wuce.
Yayin da yake magana da manema labarai a Bauchi a ranar Juma’ar nan, Damagum ya ce wannan ba shi ne karo na farko da Atiku ke barin jam’iyyar ba, yana mai cewa wannan dabi’a ce da aka saba gani a wajen Atiku tun ba yanzu ba.
A cewarsa, “Ficewar Atiku ba za ta taba zama barazana ga jam’iyyar PDP ba, kuma jam’iyyar za ta ci gaba da matsawa gaba da ƙarfi a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya.” cewar Damagum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp